Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Duk da ɗimbin jarin da aka zuba a ɓangaren wutar lantarki, babban layin lantarkin Nijeriya ya katse kusan sau 105 a ƙarƙashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu da magabacinsa, Muhammadu Buhari.
Wani bincike da aka gudanar a ranar Lahadi ya nuna cewa Nijeriya ta samu kusan lamuni 10 da darajarsu ta kai dala biliyan 4.36 daga Bankin Duniya a cikin shekaru goma da suka gabata domin tunkarar manyan ƙalubale a ɓangaren wutar lantarki.
Duk da cewa ba dukkanin lamuni 10 na Bankin Duniya aka biya gaba ɗaya ba, Gwamnatin Tarayya da sauran hukumomin ƙasa da ƙasa sun tallafa wa ɓangaren wutar lantarkin ƙasar nan da kuɗi.
Sun bayar da biliyoyin Naira don gyara masana’antar amma duk da waɗannan kuɗaɗe, fannin na ci gaba da durƙushewa, ganin yadda babban layin ke yawan katsewa wanda a lokuta da dama ya jefa ƙasar cikin duhu.
Buhari da Tinubu, ‘yan jam’iyyar APC, sun yi alƙawarin mayar da al’amura yadda ya kamata a fannin wutar lantarki.
Sai dai bisa ga dukkan alamu ƙalubalen ɓangaren wutar lantarkin ya yi ƙamari bayan gwamnatin Buhari ta karɓi mulki a hannun tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan na jam’iyyar PDP.
Bayanan da aka samu daga majiyoyi daban-daban ciki har da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya, sun nuna cewa wutar lantarkin ta katse kusan sau 93 a mulkin Buhari na shekaru takwas, daga watan Yunin 2015 zuwa Mayu 2023.
