An soke tafiyar Shettima zuwa taron Samoa sakamakon tsaiko da jirginsa ya samu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ba zai samu halartar taron ƙasashen masu tattalin arziƙi (Commonwealth Heads) ba da za a yi Samoa, kamar yadda aka tsara.

Ofishin shugaban ƙasa ya sanar hakan jim-kaɗan bayan wani abu ya yi karo da jirginsa a wani filin jiragen sama na New York da ke Amurka wanda hakan ya sa aka soke zuwan Shettima taron.

A saboda haka ne aka samar da wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Ministan Kula da Muhalli, Balarabe Lawal wadda za ta wakilci Nijeriya a taron, kamar yadda wata sanarwa da Mai taimaka wa shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar ta nuna.

A ranar Lahadi da ta gabata ne Shettima ya bar Abuja don halartar taron a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda a sanadiyyar fashewar wani yanki na gilashin jirgin ya sanya aka soke zuwansa taron.

An fara taron na wannan shekarar ne a ranar 21 ga watan Oktoba wanda kuma za a kammala a ranar Asabar, 26 ga wata.

Za a gudanar da zaɓen Sakatare-Janar na taro na gaba da kuma tattauna muhimman batutuwa da suka ƙasashen suka haɗu a kai don samun cigaba mai ɗorewa a yankunansu.

By Babaji