Yadda sojoji suka yi wa ‘yan bindigar da suka lalata babban layin lantarkin Arewa luguden wuta 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani hoton tauraron ɗan’Adam ya nuna yadda aka yi rugu-rugu da wani yanki da ke zagaye da tashar wutar lantarki da ke Shiroro inda a kwanakin baya aka samu matsalar lalacewar baban layin wutar rarraba lantarki a wurin mai ƙarfin 330Kɓ ta Shiroro-Mando.

A ranar Litinin ne Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta harba bamabamai ga ‘yan ta’addan da suka hana gyaran wutar lantarkin layin wuta na Shiroro-Kaduna da ake zargin ‘yan bindiga da lalatawa.

Lalacewar wannan layin wutar lantarki dai ya jefa al’ummar yankin Arewa cikin matsanancin duhu duk da cewa an dawo da wutar a yanzu a wasu sassa na yankin bayan umarni da Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi.

Shugaban ya ba da umarni ga jami’an tsaro da kare ma’aikatan wutar lantarki da ke aikin gyaran layin wutar.

Wannan harin bam da rundunar sojin ta kai na zuwa ne bayan mako guda da mataimakin shugaban majalisar dattawa ya bayyana cewa akwai wasu ‘yan bindiga da suka fara ƙoƙarin mamaye inda babban layin wutar ya samu matsala, inda ya ce ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na yin duk mai yuwuwa domin magance wannan matsala.

A cewar jaridar Punch, daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin saman Nijeriya, ya bayyana cewa sun samu bayanan sirri da ke tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun fara komowa wurin da aka samu matsalar lalacewar babban layin lantarkin domin hana ma’aikatan wuta yin aikinsu.

Mr Akinboyewa, ya ce a ranar 1 ga watan Nuwamba ne Rundunar sojin saman ta kai wasu hare-hare ta sama kan wuraren da ‘yan bindigar suka fara ya da sansanin su dake dajin Alawa na ƙaramar hukumar Shiroro.

Ya ce wannan hari na da nasaba da ƙoƙarin da ake yi na ganin an dawo wa da yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan Arewa wuta.

Sannan rundunar ta ce ta yi nasarar kama wasu daga cikin ‘yan bindigar tare da ƙwace kayayyakinsu.

Mista Akinboyewa, ya ce rundunar ta yanke shawarar ƙaddamar da wannan hari ta sama ne domin gujewa lalata tashar wutar daga hare-haren da ka iya shafar wurin.

Sannan ya ce rundunar sojin saman ma cigaba da gudanar da sa-ido a yankin domin magance sake taruwa ‘yan bindigar a wannan waje da kayayyakin da ake da su domin tabbatar da an dawo da yankin Kuduna da sauran jihohin Arewa wuta sosai.

Layin rarraba wutar lantarki mai ƙarfin 330Kɓ da ke Shiroro-Kaduna da ke haɗe da tashar wutar lantarki ta Shiroro da ke aiki da madatsar ruwa ta Zungeru.

Sai dai da yawa daga cikin al’ummar yankin kamar ƙungiyar mazauna yankin Shiroro a jihar Neja, sun sha neman a musanya sunan madatsar ruwan daga Zungeru zuwa Shiroro saboda madatsar a Shiroro take ba Zungeru ba.

A satin da ya wuce, gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin kawo ƙarshen rashin wuta da ake fama da ita amma Manhaja ta gano cewa jami’an tsaro sun gamu da matsalar tsaro wanda ya hana su samun damar isa zuwa madatsar ruwan. Hakan na nuna cewa akwai wahala a iya kammala aikin a cikin lokacin da shugaban ƙasa ya yi alƙawari.

Wakilinmu ya gano cewa wannan hari ya shafi ƙauyuka 12 tsakanin jihohin Kaduna da Neja inda a nan ne ‘yan bindiga ke ƙoƙarin hana ruwa gudu na dawo da wutar lantarki.

A cikin ƙayukan 12, kusan 6 suna jihar Neja ne da kuma suke kusa da tashar wutar lantarkin ta Shiroro da madatsar ruwan Zungeru.

Duk da cewa wurare kamar Birnin Gwari, Manini and Chikun na yankin Kaduna, amma rundunar ta kai harin ne saboda amfani da wuraren da suke wajen kai wa mutanen yankin hare-hare.

Sannan akwai garuruwa 6 — Kurebe, Iburo, Malfa, Galadima Kogo, Chukuba and Kwaki — da ke ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga.

Ga misali akwai ƙungiyar Boko Haram da aka fi sani da Jama’tu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad (JAS) da wata abokiyar burminta ta ISWAP waɗanda suka mamaye yankin Allawa. Sannan hare-hare da aka kai yankin sun kai ga sanadiyyar mutuwar mutanen da yara da ke yankin.

A kwanakin baya sai da Boko Haram (JAS) ta faɗaɗa ikonta a dajin Allawa inda suke kai hare-hare ga garuruwa da ke kusa da su kamar Kwaki, Chukuba, Iburo, Galamida Kogo da Malfa. Haka ma ‘yan bindiga da suka haɗa da yaran Dogo Gide sun matsa wa wannan wuri da sace musu amfanin gona.

Wani jagoran matasan Shiroro, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce wata matsala da za ta kawo cikas wajen gyaran wutar shi ne rashin hanyoyi masu kyau duk da ya ce akwai wasu wurare da ake da wutar lantarki a garin.

“Ba za ka iya zuwa wurin ba, sai dai ka yi amfani da babur ko kuma jirgi mai saukar ungulu kamar yadda suke yi idan suna turo wutar daga babban layin.

A cewar wani rahoto na Blueprint, janar-manaja mai kula da tashar rarraba wutar lantarkin Shiroro, Maiwada Paiko, ya ce a watan Disambar 2023, ‘yan bindigar sun yi barazanar ƙwace iko da tashar wutar.

Sannan ya bayyana yadda aka sace wasu ma’aikatansu a shekarar 2022 suka rasa rayukansu a yayin da jami’an tsaro ke raka ma’aikatan hukumar zuwa yankin domin gyaran lahin wutar Shiroro-Kaduna bayan wani kwautan ɓauna da suka yi musu.

By ukarofi