Trump ya roƙi masoyansa su biya wa Jam’iyyar Democrat bashin dala miliyan 20 na yaƙin neman zaɓe

Spread the love

Zaɓaɓɓen Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya buƙaci magoya bayansa da su taimaka wajen rage kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe na Jam’iyyar Democrat.

Trump ya yi wannan roƙo ne a cikin wani saƙon da ya wallafa a ɗ, a ranar Lahadi, 10 ga Nuwamba, 2024.

Shugaban ya bayyana cewa, duk da ƙoƙarin tattara kuɗaɗe a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2020, an bar ‘yan jam’iyyar Democrat da ƙarancin kuɗaɗe bayan rashin su.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya ce, yaƙin neman zaɓensa ya rage “kuɗi mai yawa” a cikin ma’ajinsu saboda yawancin yadda ya samar kafafen yaɗa labarai cikin sauƙi.

“Na yi matuƙar mamakin yadda ‘yan jam’iyyar Democrat, waɗanda suka yi gwagwarmaya da jajircewa a zaɓen shugaban ƙasa na 2020, suka tara maɗudan kuɗaɗe, amma a ce ba su da wasu maƙudan kuɗaɗe da suka rage, yanzu dillalai da sauran su ne ke matse su,” Trump ya rubuta.

“Duk abin da za mu iya yi don taimaka musu a cikin wannan mawuyacin lokaci, ina ba da shawarar da mu yi, a matsayinmu na Jam’iyya kuma saboda tsananin buƙatar haɗin kai,” inji shi.

Rahotanni sun nuna cewa, an kammala kamfen ɗin Kamala Harris da kusan dala miliyan 20 na bashi, a cewar majiyoyin da shugaban ofishin Politico na California, Christopher Cadelago ya ruwaito.

Na yi mamaki sosai cewa ‘yan jam’iyyar Democrat, waɗanda suka yi yaƙi mai ƙarfi da jajircewa a zaɓen shugaban ƙasa na 2020, suka tara adadin kuɗi da yawa, ba su da sauran ‘yan daloli da yawa. Yanzu haka suna matse. Duk abin da za mu iya yi don taimaka musu mu yi,” inji Trump. 

Duk da tara sama da dala biliyan 1, Harris ta ƙare da dala miliyan 118 kawai a cikin kuɗin yaƙin neman zaɓe a tsakiyar Oktoba.

Harris, ‘yar takarar Democrat a zaɓen Nuwamba 5, ta kafa sabbin bayanan tattara kuɗaɗe tare da yaƙin neman zaɓenta da Super PACs masu alaka, waɗanda suka tara dala biliyan 2.3, tare da kashe dala biliyan 1.9.

Saɓanin haka, yaƙin neman zaɓen Trump ya tara ya kuma kashe kaɗan, inda aka samu dala biliyan 1.8 da kuma kashe dala biliyan 1.6.

“Muna da kuɗaɗe da yawa da suka rage a cikin babban akawun ɗinmu na yaƙin neman zaɓe, kuma hakan ba ya nufin ba mu kashe kuɗi sosai ba,” cewar Trump. 

Ajay Jain Bhutoria, fitacciyar mai tara kuɗaɗe ga Harris, ta yi bayanin cewa yayin da kamfen ɗinta ya samu gagarumin tallafin kuɗi, ta yi ƙoƙarin daidaita ƙididdigar kuɗaɗen da kuma yadda aka kashe su.

By ukarofi