Fargaba kan ƙaruwar mutuwar fuji’a a Nijeriya

Spread the love

A cikin ’yan kwanakin nan, Nijeriya na fuskantar wani yanayi mai tada hankali kan ƙaruwar mace-macen fuji’a – mutuwar ba zato ba tsammani – a tsakanin ‘yan ƙasarta. Wannan al’amari ya jefa iyalai da al’ummar ƙasa baki ɗaya cikin wani hali na firgici da baƙin ciki da kuma ɗimuwa.

Duk da kowa ya san cewa duk mai rai sai ya ɗanɗana mutuwa amma akan shiga wane hali na kaɗuwa da ɗimauta idan wani makusanci ya mutu ba tare da tsammani ko kuma alama ba.

A mafi yawan lokuta an fi alaƙanta mutuwa ga waɗanda ke fama da cuta ko kuma waɗanda suka tsufa.

To sai dai ba kodayaushe ne hakan ke faruwa ba, domin akan samu matasa da yara da kuma jarirai waɗanda ke rasuwa ba zato, ba tsammani.

To amma babban abin da ya fi tayar da hankali shi ne lokacin da mutum mai lafiya da kuzari ya faɗi ya mutu ba tare da nuna wata alamar kasancewa cikin rashin lafiya ba, ita ake kira da mutuwar fuji’a.

Wani ƙwararren likitan zuciya ya ce, duk da cewa a zahiri al’umma ba za su ga abin da ya yi sanadiyyar mutuwar wanda ya yi mutuwar fuju’a ba, amma zai iya yiwuwa ta samo asali daga wasu cututtukan da ba su bayyana alamominsu a zahiri ba.

Akasari abubuwan da suka fi haifar da mutuwar fuju’a na da alaƙa ne da matsalar gazawar zuciya ko kuma rashin isasshen jini a cikin ƙwaƙwalwa.

Likitan ya jero wasu larurori da suke iya haddasa mutuwar fuju’a kamar;

Rikicewar bugun zuciya:

‘Arrhythmias’ wani yanayi ne da ke shafar bugun zuciyar ɗan Adam. A irin wannan yanayi zuciya kan ƙara sauri ko kuma ta riƙa bugawa a hankali sosai.

Bugun zuciyar mutum kan ƙara sauri a lokacin da yake motsa jiki ko kuma ya ragu a wasu lokutan amma idan abin ya tsananta zai iya haifar da babbar matsala.

Abubuwan da kan haifar da mummunan sauyin bugun zuciya sun haɗa da shan miyagun ƙwayoyi, sauyi mai yawa a yawan sanadarin pH a jikin ɗan adam, da matsalar zuciya mai muni da kuma matsalar saurin bugun zuciya.

Sai dai likitan ya ce, akwai mutanen da ake haihuwar su da matsalar saurin rikicewar bugun zuciya.

Ya ƙara da cewa, “abu kaɗan sai ya sa bugun zuciyarsu ya rikice. Hatta damuwa wadda ba ta taka ƙara ta karya ba kan iya rikitar da bugun zuciyarsu, inda lamarin ke iya sanya wa zuciya ta ƙame, tare da daina bugawa.

“Da zarar zuciya ta tsaya lokaci guda za a samu mutuwa.” inji shi.

Rashin isar jini zuwa cikin zuciya:

‘Acute myocardial infraction’ a Turance, na faruwa ne a lokacin da aka samu raguwar isar jini zuwa cikin zuciya, wanda kan haifar da ƙarancin iska a cikin zuciya da rage ƙarfin zuciya wajen tura jini ga sassan jiki. Wannan matsala ce ke haifar da lalacewar sassan zuciya, lalacewa ta dindindin.

Waɗannan na ɗaya daga cikin manyan sanadim mutuwar fuju’a.

Wasu daga cikin abubuwan da suke haifar da wannan matsala sun haɗa da shan taba, da ciwon sukari, da hawan jini, da ƙibar da ta wuce kima, da rashin motsa jiki, da kaɗuwa da shan miyagun ƙwayoyi.

‘Cerebroɓascular accident’ wanda akan kira shi da ‘Stroke’ shi ne lokacin da jini ya kasa isa zuwa cikin wani ɓangare na ƙwaƙwalwa ko dai sanadiyyar toshewar jijiya ko kuma fashewar jijiyar. Wannan yanayi kan sanya wasu daga cikin ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa su mutu.

Rashin samun kulawa cikin gaggawa zai iya haifar da lalacewar ƙwaƙwalwar baki ɗaya.

Wasu daga cikin alamun bugun jini sun haɗa da jiri, da rashin iya magana da kyau, da rashin fahimtar abin da wasu ke faɗa, da rashin gani da kyau da ciwon kai nan take.

Toshewar huhu:

Wannan kan samo asali ne daga toshewar jijiya a wani ɓangare na jikin ɗan adam, musamman ƙafa, inda gundulmin kan tafi zuwa cikin huhu ya toshe hanyar ficewar jini ta cikin huhu.

Wannan kan haifar da mutuwar ɓangaren huhu da lamarin ya shafa, wanda hakan zai hana huhu ya samar da iska ga sauran sassan jiki.

Hakan na iya yin barazana ga rayuwa matuƙar ba a ɗauki mataki cikin hanzari ba.

Lamarin zai iya tsayar da bugun zuciya ko kuma rikirkita harbawar jini daga cikin zuciya.

Kashi ɗaya cikin uku na waɗanda ke samun kansu cikin wannan yanayi na mutuwa.

Alamomin mutuwar fuju’a:

Da yawa mutanen da kan fuskanci mutuwar fuju’a a mafi yawan lokaci ba su cika kokawa kan wata rashin lafiya mai tsanani ba.

Wasu kuma kan koka kan fuskantar ciwon ƙirji, ko numfashi sama-sama, ko bugun zuciya da sauri.

Shi ya sa masana lafiya ke ganin cewa ya kamata a riƙa lura sosai da mutanen da ke fuskantar larurori da suka shafi zuciya duk ƙanƙantar matsalar.

Duk mutumin da ya gamu da ɗaya da cikin matsalolin da ke janyo mutuwar fuju’a kamar yadda likita ya yi bayani, to ba abin da yake buƙata da ya wuce a garzaya da shi asibiti.

Sai dai kafin kaiwa ga asibiti ko samun likita da zai kula da shi, marar lafiyar na buƙatar kulawar gaggawa ta farfaɗo da aikin zuciyarsa wadda a sau da dama take tsayawa da aiki a yayin da mutum ya samu kansa a wannan yanayi.

Dole ne gwamnatin Nijeriya, ɓangaren kiwon lafiya, ƙungiyoyin farar hula, da ɗaiɗaikun jama’a su haɗa kai don shawo kan wannan lamari.

A mahangar Jaridar Blueprint Manhaja, yawan mace-macen fuji’a – mutuwar ba zato ba tsammani – a Nijeriya na buƙatar kulawar gaggawa. Ta hanyar magance sanin abin da ya dace, za mu iya rage afkuwar waɗannan munanan al’amura da gina al’umma mafi ƙoshin lafiya da aminci.

By ukarofi