Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta ce akwai buƙatar zuba hannun jari na Dala miliyan 10 ta hanyar haɗin guiwa tsakaninta da kamfanoni masu zaman kansu domin samar da wuta ta awanni 24.
Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana haka a lokacin da ziyarar da daraktan hukumar kula da ayyukan inganta rayuwa da haɗin guiwa ta ƙasa (ICRC), Jobson Ewalefoh, ya kai masa.
A cikin wani saƙo na bayan taro da muƙaddashin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na hukumar ICRC, Ifeanyi Nwoko, ya ba wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa, (NAN).
A cikin saƙon, mista Adelabu ya ce gwamnati kaɗai ba za ta iya samar sa Dala biliyan 10 ba saboda ɗimbin ayyuka da ke gabanta a sauran ɓangarori.
“Gwamnati ba za ta iya ba ita kaɗai, akwai buƙatar shigowar kamfanoni masu zaman kansu, sai dai gwamnatin za ta cigaba da kula da ɓangaren.
“Wannan ce ta sa hukumar ICRC ta shigo cikin lamarin saboda muna da buƙatar haɗa kai da da kamfanoni masu zaman kansu kuma hanya mafi dacewa ita ce ta hanayar ƙulla yarjejeniya,” ya faɗa.
Shi ma Mista Ewalefoh ya ce akwai buƙatar haɗin guiwa tsakanin kamfanoni masu zaman kasu da domin farfaɗo da ɓangaren wutar lantarki.
Ya ce la’akari da muhimmancin lantarki ga cigaban tattalin arziƙin, akwai buƙatar kula da kayan lantarkin da kuma kashe kuɗin wajen samar da wasu.
Shugaban ICRC ya ce ƙalubalen ɓangaren wuta na da yawa kuma sun fi ƙarfin a ce gwamnatin tarayya ce kaɗai za ta ɗauki nauyinsu.
Sannan ya ce hukumar za ta sa hannu wajen amfani da tsare-tsarenta wajen jawo kamfanoni masu zaman kansu domin haɗa Naira biliyan 10 da ake buƙatar domin samar da tsayayyiyar wutar lantarki.
Haka kuma akwai yuwuwar ICRC ta jawo masu zuba hannun jari daga ƙetare da ma sauran ɓangarorin domin farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya.
“Farfaɗo da ɓangaren lantarki abu ne da ke buƙatar tsari da zuba hannun jari da ke buƙatar lokaci. Don haka, akwai buƙatar hadin guiwa domin warware ƙalubalen da ake fama da su.”
Ya kuma yaba wa ministan kan irin ƙwazonsa a wannan bangare da yaba wa matakin da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya ɗauka.
Sannan ya ce a ƙoƙarin bunƙasa zuba hannun jari na haɗin guiwa kamar yadda Shugaban ƙasa ya buƙata, hukumar ta miƙa wasu tsare-tsare shida wanda zai kula da tafi da ayyukan haɗaka tsakanin gwamnati da sauran kamfanoni.
Shugaban ya yi jan hakali kan cewa hukumar ba za ta sassauta tsauraren ƙa’idojinta ba, domin ba za ta lamunci gazawa daga kamfanonin da suka ƙulla wata yarjejeniya ba..
