An yi naɗin Chiroman Kano kan cancanta – Uwa Matar Ɗansanda 

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano 

Hajiya Uwa Matar Ɗan Sanda, Sarkin Guɗar Giwa matar Sarkin Kano, ta bayyana naɗin da aka yi wa ɗan Sarkin Kano, Muhammad Sanusi, a matsayin Chiroman Kano da cewa, an yi akan dacewa da cancanta.

Ta ce, Chiroma yana koyi da mahaifinsa, don jama’a da akhairi da kyauta da karrama ɗan’adam da yin bajinta duk ya gada yana yi.

Ta yi kira ga al’ummar Kano su haɗa kai da bai wa gwamnatin jihar ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf goyon baya ajiye duk hayaniya saboda a kyautata baya na ‘ya’ya da jikoki su riƙa koyi da abin arziki da aka bar musu.

Ta yi nuni da cewa karamci da adalci da kyautatawa ɗan’adam haka aka san Kanawa a kai, don haka a baiwa masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin Malam Muhammad Sanusi II da Gwamnatin Kano ta Abba Kabir haɗin kai da goyon bayan don samun nasarar sauke nauyi na zaɓen da aka yi masa.

Hajiya Uwa Matar ɗansanda ta taya bayyana farin cikinta bisa irin karamci da al’umma daga sassan kasar nan suka nunawa jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da  halartar ɗaurin auren ‘yar sa da ɗan Mangal da aka yi. 

Uwa Matar ɗansanda ta ce suna addu’a da fatan da izinin Allah Kwankwaso sai ya zama shugaban ƙasar Nijeriya kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf sai ya yi wa’adi biyu a Gwamnan jihar Kano saboda kyawawan manufofinsa na son cigaban jihar Kano.

By ukarofi