Nijeriya na asarar Dala biliyan 1.1 a duk shekara saboda zazzaɓin cizon sauro

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce Nijeriya na yin asarar sama da dala biliyan 1.1 a duk shekara sakamakon zazzabin cizon sauro, wanda ke yin tasiri sosai ga tattalin arzikin kasa.

Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate ne ya bayyana hakan a yayin taron kaddamar da shirin kawar da zazzabin cizon sauro a Nijeriya (AMEN) a Abuja.

Farfesa Pate ya bayyana cutar zazzabin cizon sauro ba kawai matsalar lafiya ba ce, matsala ce ta tattalin arziki da ci gaban da ya kamata a magance cikin gaggawa.

Ya ƙara da cewa Nijeriya ce ke da kashi 27 na masu fama da cutar zazzaɓin cizon sauro a duniya, da kuma kashi 31 na mace-macen da ke da nasaba da zazzabin cizon sauro a duniya.

Ya ce a shekarar 2022 kadai, sama da yara 180,000 ’yan kasa da shekara biyar a Nijeriya ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar zazzaɓin cizon sauro, bala’in da za a iya karewa.

Ministan ya ce ƙaddamar da kwamitin ba da shawara wani shiri ne na gwamnati don magance matsalolin da suka danganci cutar da illarta ga cigaban lafiya da tattalin arziki.

By ukarofi