Google, Meta da TikTok sun biya Nijeriya harajin tiriliyan N2.55 a 2024

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanonin dijital na ƙasashen waje da ke aiki a Nijeriya, da suka haɗa da Google, Microsoft, da TikTok, da dai sauransu, sun biya Gwamnatin Tarayyar Nijeriya jimillar harajin Naira Tiriliyan 2.55 a farkon rabin shekarar nan.

Hukumar bunƙasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata ta hannun daraktar sashen sadarwa da hulɗa da manema labarai, Hadiza Umar, inda ta nakalto bayanai daga Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta Tarayya (FIRS) da Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS).

NITDA, musamman, ta yaba wa Google, Microsoft, manhajar ɗ, da TikTok saboda bin ƙa’idar aikin Intanet a Nijeriya.

Sanarwar da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) da Hukumar Kula da Watsa Labarai ta ƙasa (NBC) da NITDA suka fitar a haɗin gwiwa ta ce waɗannan biyan haraji ya ƙara inganta harkokin yanar gizo a Nijeriya.

Yayin da take bayyana tasirin hakan, NITDA ta bayyana cewa hakan ya kuma ƙara haɓaka kuɗaɗen shiga na gwamnati ta hanyar biyan haraji daga kamfanonin dijital.

By ukarofi