Shugaban Amurka Joe Biden a ranar Lahadin da ta gabata ya bayar da afuwa a hukumance ga ɗansa Hunter, wanda ke fuskantar hukunci a kan wasu laifuka biyu, duk da tabbacin da ya ba shi cewa ba zai sa baki a cikin matsalolin shari’a ba.
“Babu wani mai hankali da zai kalli gaskiyar lamarin Hunter da zai iya cimma wata matsaya, saidai kawai an zurfafa ne kawai saboda ɗana ne, kuma hakan ba daidai ba ne,” inji shugaban a cikin wata sanarwa.
Wannan matakin dai tabbas zai kawo sabon bincike kan ‘yancin tsarin shari’ar Amurka, musamman a daidai lokacin da shugaban ƙasar mai jiran gado Donald Trump ya matsa ƙaimi wajen naɗa mutanensa a hukumar ta FBI da kuma ita kanta ma’aikatar shari’a.
An yanke wa matashin ɗan Biden hukunci a farkon wannan shekarar kan yin ƙarya game da amfani da muggan kwayoyi lokacin da ya sayi bindiga wanda ya kasance laifi, kuma ya amsa laifinsa a wata shari’ar kan ƙin biyan haraji, amma bai fuskanci hukunci ba.
Joe Biden, wanda ke cikin makonnin ƙarshe na shugabancinsa kafin Trump ya karɓi ragamar mulki a ranar 20 ga watan Janairu, ya sha cewa ba zai yafewa ɗansa ba.
“Na ce ba zan yi katsalanda ga shawarar da ma’aikatar shari’a ta yanke ba, kuma na cika alƙawari duk da cewa na kalli yadda ake masa kallon matsayinsa na ɗana, kuma aka kasa yi masa adalci,” inji Shugaba Biden a wata sanarwa ta Lahadi.
Ya ƙara da cewa “Tuhumar da ake tuhumarsa da ita ta biyo bayan wasu ‘yan adawa na siyasa a majalisa sun tunzura su su kawo min hari tare da adawa da zaɓena.”
“Na yi imani da tsarin shari’a, amma kamar yadda na koka da wannan, na kuma yi imanin cewa zaren siyasa ya mamaye wannan tsari, wanda ya haifar da rashin adalci.”
Yafewar ta zo ne a yayin da aka kai ƙarshen shari’ar laifuka kan zaɓaɓɓen shugaba Trump bayan da kotun ƙoli ta yanke hukunci kan kariyar da shugaban kasa yake da shi a hukumance wadda ta ba da tabbacin cewa, abokin hamayyar Biden na jam’iyyar Republican ba zai taɓa ganin gidan yari ba, koda kuwa laifukan da ake tuhumarsa na ƙarya kan bayanan kasuwanci a watan Mayu sun tabbata.
