An halasta wa karuwai hutun haihuwa da fensho a Belgium

Spread the love

A ranar Lahadin da ta gabata ne Belgium ta zartar da wata muhimmiyar doka da ta bai wa karuwai haƙƙi daidai da sauran ma’aikata.

Sabuwar dokar ta tabbatar da cewa, za a ɗauki karuwai a matsayin ma’aikata, wanda hakan zai ba su damar samun fa’idodi kamar hutun haihuwa, gudunmawar fansho, da kariya ta doka daga cin zarafi.

An yanke shawarar ne sakamakon zanga-zangar watanni da aka shafe ana yi a shekarar 2022, sakamakon rashin tallafin jihohi ga karuwai yayin iftila’in cutar Korona.

Wannan sauyin da aka samu, wanda ya kasance irin sa na farko a tarihin dokar duniya, zai ba wa karuwai gurbi a ma’aikatun ƙasar, wanda hakan zai ba su damar morar duk wata kariya da ma’aikaci zai samu, kamar kariyar aiki.

Har ila yau, dokar ta ba da babbar kariya ga ma’aikata masu sana’ar karuwanci, da ba da tabbacin yancin zaɓar abokin mu’amala, bijirewa wani abu da kwastomomin suka buƙata daga gare su wanda ba su da ra’ayi, ko dakatar da wani abu da ake ƙoƙarin yi a jikinsu a kowane lokaci.

Bugu da ƙari, masu ɗaukar karuwai dole ne su cika ƙayyadaddun ƙa’idodi, waɗanda suka haɗa da; adireshin wurin aiki a Belgium, kiyaye doka da kuma ɗabi’a mai kyau, tabbatar da wuraren kai karuwan suna da tsaro, tsafta da kuma tanadar kwararon roba.

ƙungiyar kare haƙƙin karuwai ta Belgium ta ce, dokar “babban ci gaba ce, ta kawo ƙarshen wariyar da ake yi wa karuwai. “

Sophie, wata karuwa a Belgium, ta shaida wa BBC cewa, sabuwar dokar “dama ce a gare mu ta zama a matsayin mutane.”

By ukarofi