Paparoma Francis ya yi kira ga ‘yan siyasar ƙasar Lebanon a ranar Lahadi da su gaggauta zaɓen sabon shugaban ƙasa, domin ganin hukumomin ƙasar sun koma kan aiki.
“Ina mai kira ga ‘yan siyasar Lebanon da su gaggauta zaɓar shugaban jamhuriyar cikin gaggawa,” inji Fafaroma a dandalin Saint Peter a ƙarshen sallar Lahadin Angelus.
Ana buƙatar cibiyoyi na Lebanon su farfaɗo tare da fara aiki kamar yadda aka saba don gudanar da sauye-sauyen da suka dace da kuma ci gaba da aikin ƙasar a matsayin misali na zaman lafiya tsakanin addinai daban-daban, inji Francis.
Kakakin majalisar dokokin ƙasar Labanon, Nabih Berri, ya kira zaɓen shugaban ƙasa da za a yi a ranar 9 ga watan Janairu wani yunƙuri na kawo ƙarshen giɓin shugabanci na shekaru biyu.
Lebanon ta kasance ba ta da shugaban ƙasa tun lokacin da wa’adin Michel Aoun ya kare a watan Oktoban 2022.
Babu ɗaya daga cikin manyan ƙungoyoyin biyu a majalisar dokokin ƙasar Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran da masu adawa da ita da suka cancanta, kuma ba su da rinjayen da ake buƙata na zaɓen shugaban ƙasa kuma sun kasa cimma matsaya kan ɗan takarar da ya dace.
