Shugaban Amurka zai kai ziyara Angola 

Spread the love

A ranar 1 ga watan Disamba ne shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden, zai kai ziyara ƙasar Angola, domin jaddada ƙudurin Amurka na ƙarfafa alaƙa da ƙasashen Afirka, a ƙoƙarin ganin takwarata ƙasar Sin ba ta zarce ta a mu’amala da ƙasashen ba.

A cewar fadar White House, ziyarar ta shugaban ƙasar mai barin gado na da nufin daƙile ƙaruwar tasirin da Beijing ke da shi a nahiyar da kuma aza tubalin sabuwar hanyar kyakyawar mu’amala tsakanin Amurka da Afirka, wadda za ta ɗore har bayan wa’adin shugabancin Biden.

An yi niyar yin wannan tafiya ne a ranar 13 ga watan Oktoban 2024, saidai iftila’in Hurricane Milton ya kawo tsaiko har zuwa ranar 1 ga watan Disamba da aka yi ta.

Wani babban jami’in gwamnati ya bayyana cewa, ƙudurin Amurka game da Afirka sun canza a ƙarƙashin mulkin Biden. Domin Shugaban ya mayar da hankali sosai kan zuba jari a nahiyar maimakon dogaro da taimakon raya ƙasa na gargajiya, da tallafi da kuma agaji, kamar yadda jami’in ya shaida wa manema labarai yayin wani kira a ranar 29 ga watan Nuwamba.

Ya ƙara da cewa, wannan ne dalilin da ya sa ziyarar Biden ke da muhimmanci da kuma dalilin da ya sa aka zaɓi ƙasar Angola.

Yayin da yake can, ana sa ran Biden zai bayyana muhimmin aikinsa da aka fi sani da shirin ‘Lobito Corridor’, wanda gwamnatin ta ce yana da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin Amurka da tsaron ƙasa. Aikin zuba jarin layin dogo wanda aka ƙaddamar a shekarar da ta gabata zai bai wa Amurka damar samun ma’adinai masu muhimmanci a Afirka da kuma faɗaɗa damar tattalin arzikin Afirka.

Titin jirgin ƙasa mai nisan mil 1,000 zai ratsa ƙasashe uku, wanda zai haɗa birnin Lopino mai tashar jiragen ruwa na Angola da yankunan da ke da arzikin ma’adinai.

Daga ƙarshe layin dogo mai nisan mil 1,000 zai ratsa ƙasashe uku, wanda zai haɗa birnin Lobito mai tashar jiragen ruwa na Angola da yankunan da ke da arzikin ma’adinai na Jamhuriyar Demokraɗayyar Kongo (DRC) da kuma Copperbelt na Zambia. An yi la’akari da babban yunƙurin da Washington ke yi don tinkarar shirin jam’iyyar kwaminisanci ta Sin (CCP’s) Belt and Road Initiatiɓe (BRI) a Afirka.

Babban jami’in gwamnatin ya kuma bayyana cewa, jarin da Amurka ke zubawa ya ba da wata hanyar shiga tsakani a tsarin zuba hannun jarin da ƙasar Sin ta yi, waɗanda galibi ana alakanta su da “bautar da ƙananan yara, da cin hanci da rashawa.”

Ya ƙara da cewa, saka hannun jari a ababen more rayuwa zai iya rage lokacin da ake ɗauka don jigilar muhimman ma’adanai daga kwanaki 45 zuwa kimanin sa’o’i 45.

Biden zai kasance a babban birnin Angola, Luanda, daga ranar 2 ga watan Disamba zuwa 4 ga watan Disamba. 

Ziyarar tasa ita ce ziyarar farko da shugaban Amurka zai kai a Afirka cikin kusan shekaru goma. Shugaba George W. Bush da Barack Obama sun yi tafiye-tafiye da dama zuwa nahiyar a lokacin shugabancinsu, yayin da Shugaba Donald Trump bai yi tafiya ko ɗaya ba a wa’adin mulkinsa na farko.

Tafiyar Biden kuma za ta kasance karo na farko da wani shugaban Amurka mai ci ya ziyarci Angola.

Jami’an Biden sun yi imanin cewa yawancin ayyukansa za su ci gaba a ƙarƙashin gwamnati mai zuwa.

“Haɗakar Amurka da Afirka ta samu goyon bayan gwamnatoci da dama a baya, na tsawon lokaci, wanda ya haifar da ɗa mai ido. Kuma ina ganin hakan wata kyakkyawar al’ada ce,” inji wani babban jami’in gwamnatin yayin kiran.

Ana sa ran Biden zai gabatar da jawabi a Luondo wanda ke nuna ƙoƙarin sa na rufe giɓin ababen more rayuwa a Afirka, da faɗaɗa damar tattalin arziki, da inganta haɗin gwiwa a fannin fasaha da kimiyya a nahiyar.

A taron shugabannin Afirka na 2022, gwamnatin Amurka ta yi alƙawarin zuba jarin dala biliyan 55 a Afirka, kuma ta cika kashi 80 cikin 100 na alƙawurran zuba jari tun lokacin, a cewar fadar White House.

Biden zai kuma gana da shugaba João Lourenco na Angola yayin ziyarar tasa.

A wata hira da ya yi da jaridar New York Times kwanan nan, Lourenço ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, kamfanonin mai da iskar gas na Amurka ne kawai suka saka hannun jari a Angola, ƙasa mai arzikin man fetur. Kuma yayi fatan ziyarar Biden mai zuwa za ta taimaka wajen karkatar da jarin Amurka zuwa wasu sassa.

Ya ƙara da cewa, gwamnatin Angola ba ta da damuwa kan yiwar tasgaro a alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu a gwamnatin Trump mai jiran gado.

Lourenço ya halarci taron shugabannin Amurka da Afirka a 2022 wanda Biden ya shirya a Washington. Daga baya ya ziyarci Biden a fadar White House a watan Disambar bara.

A ziyar ta Luanda, ana sa ran Biden zai ba da sanarwar sabbin abubuwan da suka shafi sashen tsaron lafiya na duniya, noma, tsaro, da kiyaye al’adun Angola.

By ukarofi