Tsohuwar matar tsohon shugaban ƙasar Iɓory Coast Laurent Gbagbo, ta bayyana aniyar ta ta zama ɗaya daga cikin masu zawarcin kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2025.
Simone Ehivet, matar tsohon shugaban da suka rabu ta bayyana kudirinta a hukumance.
Ehivet ta samu wannan damar ta tsayawa takara ne daga jam’iyyarta ta Moɓement of Capable Generations (MGC) a yayin wani taro da ta gudanar a garinsu na Moossou da ke yankin kudu maso gabashin ƙasar.
A jawabinta yayin da aka tsayar da ita, Ehivet ta bayyana hangen nesanta game da Iɓory Coast, inda ta jaddada samar da maslaha tsakanin ƙasar ta hanyar yin afuwa mai yawa, samar da abinci, da bunƙasa masana’antu.
A cewarta, waɗannan muhimman abubuwan da za ta sa a gaba, suna da matuƙar muhimmanci ga ci gaban al’umma tare da haɗin kai.
Simone Ehivet da shugaba Laurent Gbagbo sun rabu a watan Yunin 2023 bayan sun kwashe shekaru 34 a matsayin ma’aurata, wanda hakan ya bayyana dogon tarihin fafutukar siyasa na haɗin gwiwa da ke tsakanin su.
Ehivet ta kasance tsohuwar malama, wadda ta fara fafutuka tun a farkon rayuwar jama’a a, a matsayin yar ƙungiyar haɗin kan ɗalibai a cikin 1970s.
Tafiyar siyasarta ta samu karɓuwa ne a lokacin da ta haɗu da tsohon mijinta Gbagbo a shekarar 1973, domin a tare suka kafa Jam’iyyar Popular Ivory Coast (FPI) a 1982, wadda ta ƙalubalanci gwamnatin shugaba Felix Houphouet-Boigny.
A lokacin da aka tsare Laurent Gbagbo gidan yari kan laifukan yaƙi, FPI ta samu, ƙarƙashin jagorancin Pascal Affi N’Guessan, wanda shi ma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaɓe mai zuwa, wato dai zai kara da Simone Ehivet a zaɓen 2025.
Ehivet ta shiga jerin masu neman kujerar shugaban ƙasa da zummar kafa nata tarihi a siyasar Ivory Coast, wanda hakan ya ba ta damar baje kolin ƙwarewarta wurin yin shiri da kuma sabon hangen nesa, don zage damtse a karawar ta da abokan takara.
