Kashi 70 na ’yan Nijeriya sun ƙi bada cin hanci a 2023 – ICPC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu (SAN) ya ce kashi 70 cikin 100 na ‘yan Nijeriya da aka nemi su ba da cin hanci a shekarar 2023 sun yi watsi da shi.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ke neman haɗin gwiwa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, ganin cewa babu wata hukuma zaya da za ta yaƙi cin hanci da rashawa ita kazai ba tare da goyon baya da haɗin gwiwar wasu ba.

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ya bayyana haka a Kano yayin wani taro da babban Lauyan jihar a yankin Arewa maso Yamma kan ƙarfafa ƙarfin ICPC na daƙile cin hanci da rashawa.

Taron mai taken “Kafa wata al’umma ta aiki ga Atoni Janar,” an yi taron ne da nufin samar da haɗin gwiwa na dogon lokaci wajen gina haɗin kan yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya.

Ya ce, “Babu wani ɓangare na gwamnati ko matakin gwamnati ko hukuma da zai iya yaƙi da cin hanci da rashawa saboda muna buƙatar haɗa kanmu a cikin gida da yanki da kuma ƙasashen duniya domin mu yaƙi cin hanci da rashawa. Wannan wata dama ce ta haɓaka haɗin gwiwarmu don tabbatar da cewa mun samar da tsarin riƙo da gaskiya a cikin ƙasarmu mai albarka.

“A kan haka, ina kira ga Babban Lauyan Arewa maso Yamma da ya haɗa kai da ICPC don ƙarfafa tsarin riƙon amana da gaskiya da ke yi wa jama’a hidima.

“Kodayake, duk da waɗannan ƙalubale, labari mai daɗi shi ne kashi 70 cikin 100 na ‘yan Nijeriya sun ƙi ba da cin hanci a shekarar 2023. A Arewa maso Yamma, kashi 76 cikin 100 na mutanen da suka fuskanci buƙatun cin hanci sun bijirewa mafi girman ƙima a tsakanin shiyyoyin siyasar Nijeriya, wanda hakan ke nuna adawa da cin hanci da rashawa a yankin.”

Ya bayyana cewa, ƙarfafa ƙoƙarin haɗin gwiwa yana da matuƙar muhimmanci wajen samun nasara mai ɗorewa a yaƙi da cin hanci da rashawa.

“A matsayinmu na masu ruwa da tsaki, dole ne mu ci gaba da ƙarfafa wa al’ummar Arewa-maso-Yamma kwarin gwiwar yin watsi da bukatar cin hanci. A matsayina na shugaban hukumar ICPC, na himmatu wajen ganin hukumar ta yi amfani da ƙarfin ikonta na tabbatar da doka da kuma matakan kariya da suka haɗa da neman goyon bayan jama’a wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya a cikin tsarin doka,” inji shi.

Babban Alƙalin Alkalan Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ya yaba da yadda Hukumar ICPC ta ɓullo da wani shiri na ba da fifiko ga matakan kariya don yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya.

By ukarofi