Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
’Yan ta’adda sun yi garkuwa da Honorabul Kabiru Onyene, sanannen hadimi ga tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.
A ranar Litinin ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da Hon. Kabiru a ofishinsa da ke garin Okene da misalin ƙarfe 7 na dare, bayan sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi.
Wani ganau ya ce “kwatsam muka jin harbe-harbe, jama’a sun fara guje-guje, shi ne muka gane cewa ƙarar bindiga ne.
“Bayan ’yan mintoci sai muka ji harbe-harben a wurin ofishin Kabiru, inda suka tafi da shi.
“Amma abin mamaki shi ne wurin da abin ya faru kusa yake da wani shingen binciken sojoji a kusa da gidan tsohon gwamna,” in ji shi.
A safiyar Talata wani ɗan ƙabilarsa ya wallafa a kafar sada zumunta cewa, “A taya mu da addu’a, jiya da dare an yi garkuwa da ɗan uwana Honorabul Kabiru Onyene, daga ofishinsa.
“Allah (SWT) Ya kare shi Ya kuma yi wa hukumomi jagoranci su kuɓutar da shi da wuri domin ya dawo cikin iyalansa.”
Iyalan ɗan siyasan sun ce masu garkuwar ba su tuntuɓe su ba, lamarin da ya kawo fargaba.
Mun tuntuɓi kakakin ’yan sandan jihar Kogi, SP Williams Aya, game da lamarin amma ya ce ba shi da labari, sai dai ya bincika.
Sai dai kuma har zuwa lokacin da muka kammala wannan labari ba mu ji daga gare shi ba.
