





Daga BELLO A. BABAJI
A wata gagarumar nasara ƙarƙashin gyare-gyaren da Shugaba Bola Tinubu ke yi wa ɓangaren mai a Nijeriya, kamfanin gas na ‘Oriental Energy Resources Limited’ ya fitar da Dala 316 don bunƙasa samar da man fetur a ƙasar bisa tsarin maɗaukan FPSO.
Aƙalla ganga miliyan ɗaya FPSO zai ke fitarwa wanda hakan ya ƙera adadin ganga 17,000 da ake iya samarwa zuwa ganga 30,000 a kullum.
A rabin farko na shekarar 2025 ne ake sa ran tsarin zai fara aiki a Nijeriya.
Mataimakin shugaban ƙasa, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu a yayin bikin buɗe sabon tsarin na FPSO a Dubai, ya ce hakan zai taimaka wa ƙoƙarin da shugaban ƙasar ke yi na inganta ababen more rayuwa a ɓangarori daban-daban.
A lokacin da ya ke jawabi a taron da aka shirya a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Shettima ya ce Nijeriya ta na daga cikin ƙasashen da ke tafiya da yadda zamani ya zo bisa ci-gaba da ake samu.
Ya kuma ce Nijeriya a shirye ta ke ta bi tsarin duniya wajen samun albarkatun iskar gas, ya na mai cewa an samu nasara ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu a ɓangaren mai da Gas.
Shettima ya kuma yaba wa shugaban Kamfanin ‘Oriental Energy Resources Limited’ Alhaji Muhammadu Indimi bisa nasarorin da ya samu waɗanda suka taimaka wajen samun sauye-sauye masu amfani.
Har’ilayau, Shettima ya ce samun irin jiragen dakon mai na FPSO za su taimaka wa matatun mai na gida wajen faɗaɗa adadin man da suke samarwa da kuma haɓaka tattalin arziƙi.
