NNPCL ya rage farashin fetur a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL ya rage farashin litar fetur a gidajen mai dake birnin tarayya Abuja.

Masu ababen hawa sun ce gidajen man sun rage farashin ne daga N1,060 zuwa 1,040 wanda hakan ya nuna an samu ragin Naira 20 a kowacce lita.

Hakan na zuwa ne makonni uku dawo wa aiki da matatar Fatakwal ta yi bayan tsawon lokaci da rufe ta.

By Babaji