Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya turawa Majalisar Dokokin jihar sunayen mutum shida domin ta sahale masa ya naɗa su a matsayin sabbin Kwamishinoni a gwamnatin sa.
Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Rt. Honarabul Jibril Isma’ila Falgore ne ya karanta takardar da gwamnan ya aiko a zaman majalisar na safiyar yau Litinin.
Sunayen da Gwamnan ya tura sun haɗar da tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin da akawun jihar Kano da sauran su kamar haka
- Shehu Wada Sagagi
- Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya
- Dakta Isma’il Ɗan Maraya
- Ɗahiru Muhammad Hashim
- Injiniya Gaddafi Sani Shehu
- Kwamared Abdulkadir Abdussalam.
Matakin Gwamnan dai na zuwa ne bayan da ya yi wa majalisar zartarwar sa garambawul a makon da ya gabata yayin da ya cire wasu Kwamishinoni bayan ya canza ma wasu ma’aikatu.
