Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa kan yadda kamfanin haƙar mai na Shell da abokan hulɗarsa suka amince da zuba jarin Dala biliyan biyar kan aikin haƙo ɗanyen mai a cikin teku.
A rahoton da Blueprint Manhaja ta samu, aikin shi ne babban aikin haƙo mai daga teku karo na farko tsawon shekaru masu yawa a Najeriya, sannan zai taimaka wa tsare-tsare da manufofin shugaban ƙasa na jawo hankalin masu zuba jari a fannin mai da iskar gas.
Aikin mai suna ‘Bonga North Oilfield’ zai laƙume Dala biliyan biyar, ana kuma sa ran zai riƙa samar da gangar ɗanyen mai miliyan 350. Kamfanin haƙar mai na Shell shi ke da kaso 55 kan gudanar da aikin. Sauran abokan hulɗarsa sun haɗa da kamfanin mai na ƙasa, NNPC da ExxonMobil, da TotalEnergies, da kuma Eni.
Baya da haƙar mai aikin zai kuma taimaka wajen samar da cigaba a fannin wutar lantarki, “ajandarmu ta sabunta fata ta maida hankali kan janwo hankalin masu zuba jari domin bunƙasa tattalin arziƙinmu da samar da wadata da arziƙi ga al’ummarmu. Matsayar da Shell da abokan hulɗarsa suka cimma na zuba jari a wannan aiki na haƙar mai ya tabbatar da nasarar ƙoƙarin da muke. Za mu cigaba da ba su dukkan haɗin-kai da goyon bayan da ya dace domin tabbatar da ganin an yi nasara,” inji Shugaba Tinubu.
