Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ce ta amince da sunayen mutum bakwai da gwamnan Kano Injiya Abba Kabir Yusuf ya aike domin tantancewa ya naɗa su a matsayin kwamishinoni, Kuma ‘yan majalisar zartarwar Jihar Kano.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar Lawan Hussaini cibiyar ‘Yan Gurasa ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala tantance mutanen bakwai.
In da ya ce mutanen da aka zabo nagartattu ne ƙwararru.
“Ƙwararru ne kuma matasa masu ƙwari kuma matasa masu niyyar yin aiki, kun ga yadda akai masu tambayoyi Kuma suka amsa yadda ya kamata.
Musamman akan wutar lantarki da ke ci mana tuwo a ƙwarya da kuma muhalli da dai sauransu, dukkaninsu idan an sanya su cikin ƙunshin gwamnati kwalliya za ta biya kuɗin sabulu” inji Hon. Cediyar ‘Yan Gurasa
Waɗanda aka tantance din sun haɗa da; Alh. Shehu Wada Sagagi, Alh. Abdulkadir Abdulsalam AG, Ibrahim A. Waiya, da Dakta Isma’il Ɗanmaraya da Dakta Ghaddafi Sani Shehu da Dakta Ɗahir M. Hashim da kuma mutum ɗaya da Gwamnan ya ƙara suka zama bakwai shi ne Nura Iro Ma’aji.
Majalisar dai ta ce ta turawa gwamna Abba rahoton domin bashi damar rantsar da su da kuma tura su ma’aikatun da za su yi aiki.
