Ƙaramar Hukumar Kaugama ta Jigawa za ta kewaye maƙabartu

Spread the love

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Ƙaramar hukumar Kaugama dake Jihar Jigawa, ta shirya tsaf domin inganta harkar Noma a jihar.

Shugaban ƙaramar hukumar, Alh Usman Masaki D Sule ya tabbatar wa manema labarai a Dutse ce inda ya ce ƙaramar hukumar ta ware N5,700,000,000 domin yi wa al’ummar yankin ayyukan raya ƙasa.

Ya ce ƙaramar hukumar za ta kashe kuɗaɗen ne wadda hakan yana cikin kasafin kuɗinta shekarar 2025.

Masaki ya ce za su bada fifiko ne wajen harkar kiwon lafiya, noma da inganta harkar ilimi.

Ya ƙara da cewa ƙaramar hukumar za ta tallafa wa Marasa lafiya Mata da ƙananan yara .

Ya kuma yi alwashin samar da titina da za su haɗe karamar hukumar da ƙauyuka shida dake ƙarƙashinta.

Kazalika, ƙaramar hukumar za ta gina masallatan juma’a da ƙananan masallatai a unguwanni don inganta harkokin addini.

Har’ilayau, ya ce za su inganta tsaro a ɗaukacin maƙabartun ƙaramar hukumar inda aka ware maƙudan kuɗaɗen domin kewaye wasu manya guda uku tare da samar musu da ruwa da fitilu.

An kuma ware kuɗaɗe don gyaran gidan hakiman Layo da Marke da Kayyawa.

Za kuma su yi ƙoƙarin sulhunta rikicin dake tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar tare da haɗe kai da jami’an tsaro wajen inganta tsaro.

By Babaji