Janye takunkumin haƙar ma’adanai a Zamfara zai bunƙasa tattalin arziƙin Nijeriya – Matawalle

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ce, Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da janye takunkumin hana haƙar ma’adanai a jihar Zamfara domin haɓaka tattalin arziƙin Nijeriya.

Ministan ya bayyana hakan ne a yayin wani zaman cin abinci da aka shirya wa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara a Gusau a ranar Lahadi.

Matawalle ya ce, hikimar janye takunkumin shi ne ba da dama ga masu zuba hannun jari daga ciki da wajen ƙasar nan shiga harkar ma’adanai a jihar.

Haka kuma kasancewar jihar na da tarin ma’adanai a ƙasa, janye takunkumin a cewar ministan sai ba da dama ka masu sha’awar neman lasisi shigowa harkar domin dogaro da kai.

Ya ce cigaba da haƙo gwal da sauran ma’adanai na ƙarƙashin ƙasa zai ƙara bunƙasa kuɗin shigar da jihar ke samu.

Sannan Shugaba Tinubu ya sanya sharaɗin samar da kamfanoni a jihar.

“Ta haka, ‘yan asalin jihar za su samu aikin yi tare da bunƙasa tattalin arziƙin jihar da inganta rayuwar al’ummar jihar bakiɗaya,” inji ministan.

A Yayin da yake magana kan sake fasalin haraji, Matawalle ya ce, an tsara daftarin dokar ne domin tabbatar da an samar da ƙarin kuɗin haraji ga ƙasa da jihohi bakiɗaya da kuma faɗaɗa harkokin kasuwanci.

Ministan ya jaddada buƙatar neman gwamnatin tarayya da ta kammala hanya mai hannu biyu daga ƙaramar hukumar Illela ta jihar Sakkwato zuwa Badagry ta jihar Legas.

Ya ce shakka babu wannan aiki zai buɗe ƙofofi da yawa na tattalin arziƙi ga Arewa.

By ukarofi