Farfesa Aisha Maikuɗi ta zama cikakkiyar shugabar Jami’ar Abuja

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Majalisar gudanarwar Jami’ar Abuja, ƙarƙashin jagorancin Air Vice-Marshal Saddiq Ismaila Kaita, ta amince da naɗin Farfesa Aisha Sani Maikudi a matsayin Shugabar Jami’ar ta bakwai. Wannan sanarwa ta fito ne a yayin taron majalisar na musamman karo na 77 da aka gudanar a ranar Talata, 31 ga Disamba, 2024. Naɗin ta zai fara aiki daga 1 ga Janairu, 2025, kuma zai gudana har na tsawon shekaru biyar kacal, ba tare da yiwuwar sabuntawa ba.

A cewar sanarwar da daraktan watsa labarai na jami’ar, Habib Yakoob, ya sanya wa hannu, Farfesa Maikuɗi ce ta yi fice daga cikin mutane goma da aka tantance domin wannan muƙami, bisa ƙa’idoji da dokokin da suka shafi zaɓin shugabanni a jami’ar. Tun kafin wannan naɗin, Farfesa Maikuɗi ta riƙe muƙamin a matsayin mai rikon kwarya tun daga 5 ga Yuli, 2024. A lokacin, ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da majalisar gudanarwar domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jami’ar, inda ta nuna ƙwarewa da shugabanci na ƙwarai.

An haifi Farfesa Aisha Sani Maikuɗi a ranar 31 ga Janairu, 1983, a Jihar Katsina. Ta fara karatun ta a Sacred Heart School, Kaduna, inda ta samu shaidar First School Leaving Certificate a 1993. Daga nan ta tafi Queens College, Yaba, Legas, inda ta kammala jarabawar WASSCE a shekarar 1999. Ta samu digirinta na farko a fannin Shari’a daga Jami’ar Reading a 2004, sannan ta ci gaba da karatu a London School of Economics and Political Science, inda ta kammala digiri na biyu a 2005, a fannin Shari’ar ƙasa da Ƙasa. Bayan haka, ta halarci makarantar koyar da aikin lauya ta Najeriya daga 2006 zuwa 2007, sannan ta kammala digirin digirgir (PhD) a Jami’ar Abuja a shekarar 2015.

Ta fara aiki a matsayin malama a Jami’ar Abuja a ranar 4 ga Satumba, 2008, a matsayin Lecturer II, sannan ta hau matakai har ta zama Farfesa a shekarar 2021. Wannan sabon naɗin ya ƙara tabbatar da rawar gani da ƙwarewar Farfesa Aisha Sani Maikuɗi a fannin ilimi da shugabanci, wanda zai zama alfanu ga Jami’ar Abuja da ma Ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi