Bayan ƙasa da awanni 24 da gwamnatin Australia ta shawarci ‘yan ƙasarta su sake tunani kan tafiye-tafiye zuwa Najeriya saboda dalilan tsaro, gwamnatin tarayya, ta hannun ma’aikatar harkokin waje, ta fitar da wata sanarwa ga ‘yan Najeriya da ke shirin tafiya zuwa Australia, tana gargaɗin su yi taka-tsan-tsan saboda ƙaruwar rahotannin tsangwama da wariyar launin fata da ake yi wa baƙin haure a ƙasar.
Sanarwar, wadda Kakakin ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa, ya fitar, ta bayyana cewa kwanan nan wasu birane a Australia sun fuskanci ƙaruwar hare-haren kyama da nuna bambanci ga yahudawa da Musulmai. Ma’aikatar ta ce duk da kasancewar Australia ƙasa mai fahimta da haɗin kan al’adu, wasu yankuna na fama da irin waɗannan matsaloli, wanda hakan ba zai rasa nasaba da rikice-rikicen ƙasa da ƙasa ba.
Sanarwar ta jaddada wani lamari da ya faru a farkon watan Disamba 2024 a unguwar Woollahra a Sydney, inda aka ƙona mota tare da rubuta kalaman kyama ga Isra’ila a kusa da wajen. Wannan na zuwa ne yayin da ma’aikatar harkokin wajen Australia (DFAT) ta fitar da nata gargaɗin, tana nuna damuwa kan barazanar ta’addanci, garkuwa da mutane, laifuka masu tsanani, da rashin kwanciyar hankali a Najeriya.
A martaninsa, gwamnatin tarayya ta yi kira ga ‘yan Najeriya da ke shirin tafiya zuwa Australia su kasance masu taka-tsan-tsan, su mutunta al’adun wuraren da suke ziyarta, tare da ɗaukar matakan kare kansu. Ta kuma buƙaci ‘yan Najeriya da ke fuskantar wariya ko tsangwama su tuntuɓi ofishin Jakadancin Najeriya da ke Canberra domin samun taimako. Wannan gargaɗin na da muhimmanci domin tabbatar da tsaro da walwala ga ‘yan Najeriya a ƙasashen ƙetare.
