Ina nan kan bakana – Gwamnan Bauchi ga Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya mayar da martani ga fadar shugaban ƙasa a ranar Talata, inda ya jaddada cewa ba zai janye kalamansa game da ƙudurin sauye-sauyen haraji da shugaba Bola Tinubu ya gabatar ba.

“Ba zan amince a tsoratar da ni ba a matsayin gwamna. Ina tsaye akan kalamai na. Ba domin cin mutunci ko zagi na yi ba, sai dai domin nuna gaskiya,” in ji Mohammed a cikin wata hira da aka yi da shi a shirin 2024 Year-End Review na gidan talabijin Channels wanda Blueprint Manhaja ta bibiya.

A matsayina na shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, Mohammed ya gargaɗi fadar shugaban Ƙasa da kada ta nuna girman kai, amma ta saurari jama’a. Ya bayyana cewa ƙudirin sauye-sauyen harajin, idan aka amince da shi, zai haifar da matsaloli da kuma barazanar durƙushewar jihohi da talauta su. “Ya kamata shugaba na ƙasa baki ɗaya ya saurari jihohi, ba wai ya nuna girman kai ko rashin mutunci ba, cewa duk abin da ya faru, za su ci gaba,” in ji Mohammed.

Gwamnan ya bayyana cewa matsayar fadar shugaban Ƙasa game da sauye-sauyen harajin ba ta da dimokuraɗiyya ba, yana mai cewa ko waɗanda suka fito daga ɓangaren soja za su saurari jama’a domin gyara inda ake shakku da rashin fahimta a ƙudirin.

Mohammed ya kuma soki tsarin da ke fifita wasu yankuna kan wasu a ƙudirin. Ya gargaɗi cewa ba za a bar wasu jihohi su durƙushe kawai don ba su da hedkwatar kamfanoni ba.

Mohammed da sauran gwamnonin Arewa 18 sun bayyana rashin amincewarsu gaba ɗaya da sauye-sauyen harajin Tinubu, wanda ke ci gaba da jawo cece-kuce tun bayan gabatar da shi a majalisa. Duk da haka, Tinubu ya dage cewa sauye-sauyen harajin za su tabbata.

By ukarofi