
Daga BELLO A. BABAJI
Mai bai wa Shugaban ƙasa shawara kan Harkar Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribaɗu ya ƙaddamar da shirin yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Nijeriya.
Hakan na zuwa ne bayan an kama fiye da kwantena 250 na haramtattun ƙwayoyi a wasu tashoshin jiragen ruwa na Najeriya.
Kwantena 250 na ƙwayar Tramadol da wasu abubuwa masu haɗari aka kama a tashoshin ruwan Nijeriya, kamar yadda Blueprint Manhaja ta ruwaito.
Lamarin da ya sa Mallam Ribaɗu ya ayyana yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar a matsayin barazana ga kwanciyar hankali da zaman lafiyar al’umma.

An kafa kwamiti ne, wanda ya ƙunshi hukumomi da dama da suka haɗa da ofishin NSA, Hukumar Kwastom, Hukumar Yaƙi da sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi (NDLEA), NAFDAC, da kuma rundunar Sojoji, domin binciken waɗanda suka mallaki waɗannan miyagun ƙwayoyi, tare da ƙwace su da lalata su, da kuma tabbatar da tsaron tashoshin ruwa da iyakokin ƙasar.
Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na daga abubuwan da suke haifar da munanan laifuka da rashin tsaro, waɗanda ke haifar da babban hatsari ga lafiyar jama’a da zaman lafiyar ƙasa.
Wannan yunƙuri mataki ne na wargaza hanyoyin laifuka da ake amfani da su wajen cinikin miyagun ƙwayoyi da tabbatar da aminci da walwalar ƴan Nijeriya.
