Daga UMAR GARBA a Katsina
Wasu mutane ɗauke da makamai da ake kyautata zaton ‘yan bindinga ne sun kai hari gidan shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi a Jihar Katsina, inda suka kashe wani ɗan sanda dake tsaron gidan.
Majiyar Blueprint Manhaja ta ce shugaban ƙaramar hukumar da iyalansa na cikin gidan lokacin da lamarin ya faru. Ɓarayin sun razana mazauna kewayen unguwar tare da tafka ɓarna mai yawan gaske a sassan gidan yayin harin.
Jaridar The Guardian ta tattaro daga majiya mai tushe cewa maharan sun kai harin ne da yammacin ranar Talata lamarin da ya kai ga kashe wani ɗan sanda Shamsudeen Lawal mai muƙamin kofur da ke gadin gidan shugaban ƙaramar hukumar.
Sai dai majiyarmu ba ta bayyana ko akwai wasu mutane da harin ya rutsa da su ba, amma rahotanni sun bayyana cewa yunƙurin kutsawa cikin gidan da ‘yan bindingar suka yi ya ci tura.
Malumfashi na ɗaya daga cikin ƙananan hukumoni sama da goma sha biyu (12) da ke fama da matsalar rashin tsaro a jihar, inda ake yawan samun hare-haren ta’addanci, musamman a yankunan karkara.
Har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, DSP Abubakar Aliyu bai amsa kiran da aka yi masa ba don neman ƙarin bayani.
