Jirgin Max ya yi saukar gaggawa a Kano

Spread the love

Wani jirgin saman Max Air mai rajista 5N-MBD, B733 ɗauke da fasinjoji 53 ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA) bayan ɗaya daga cikin tayoyinsa ya kama da wuta yayin sauka.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:57 na dare a ranar Talata, 28 ga Janairu, 2025, lokacin da jirgin da ya taso daga Legas ya rasa tayar gaba ta sauka. Wani daga cikin fasinjojin jirgin, Aliyu Inuwa Mansir, ya bayyana cewa tayar gaba ta kama da wuta, lamarin da ya haifar da hayaki a cikin jirgin, wanda ya tilasta su fice ta ƙofofin gaggawa.

A cewar Mansir, “Da zarar jirgin ya sauka, tayar gaba ta kama da wuta, hayaƙi ya cika cikin jirgin, kuma dole muka fita da sauri ta kofar gaggawa. Jami’an kashe gobara sun riga sun fara kashe wutar lokacin da muka fito.”

Duk da fargabar da aka samu, bayanai sun nuna cewa dukkan fasinjojin sun fita daga jirgin lafiya ba tare da wani rauni ba. Manajan Max Air a Kano, Malam Bello Ramalan, ya tabbatar da cewa an ceto kowa cikin ƙoshin lafiya.

By ukarofi