Ta’addanci: Gwamnatin Tarayya ta duƙufa wajen kawo zaman lafiya a Tafkin Chadi – Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu a shirye take wajen haɗe kai da gwamnonin ƙungiyar yankin Tafkin Chadi da wasu masu-ruwa-da-tsaki wajen kawo zaman lafiya mai ɗorewa a yankin wanda mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka jima suna addabar sa tsawon shekaru.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana hakan a yayin taron ƙungiyar karo na 5 da Gwamnatin Jihar Yobe ta jagoranta a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

An gudanar da taron ne musamman don tattauna batutuwan da suka shafi tsaro, haɗin kai tsakanin yankunan iyakoki da ci-gaba da aka samu da kuma rashin daidaito da damammaki acikin matasa a sakamakon ayyukan ta’addanci.

Shettima ya ce an samar da ƙungiyar ne ba kaɗai don warware ƙalubalen da yankin ke fuskanta ba, har ma da manufofin haɗin-gwiwa don cimma buƙatu na ci-gaba.

Ya kuma yaba wa mambobin ƙungiyar ganin yadda suke ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunansu, ya na mai musu fatan nasara da samun ci-gaba mai ɗorewa.

A nasa jawabin, shugaban taron kuma Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya yaba da halarta daga ofishn Shugaban ƙasa da suka samu tare da jinjina wa ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya wajen bada gudunmawa a yaƙar ta’addanci a yankin.

Ya kuma jaddada muhimmancin ƙarfafa alaƙa tsakanin jihohin ƙungiyar, ya na mai cewa za su yi ƙoƙarin samar da damammaki da za su amfanar da al’ummar yankin.

By Babaji