Littafin ‘Gawa Ta Ƙi Rami’ ya bankaɗo illolin cin amana da rashin gaskiya

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Lokacin da na kammala karanta littafin Gawa Ta ƙi Rami’ na Ayuba Muhammad ɗanzaki, abin da ya fara faɗo min a rai shi ne, ‘Ga fa magajin Bala Anas Babinlata da Nazir Adam Salihi!’ Na faɗi haka ne kuwa bisa lura da na yi da irin salon labarin da marubucin ya tsara. Labari ne da a turance ake kira da ‘thriller’ wato salon ‘ƙirji-ɗarɗar’, kamar yadda aka yi masa fassara da Hausa. Shi wannan salo yana zuwa ne a yanayin labari mai ɗauke da rikita-rikita, tsoratarwa, fargaba, kwamacala, wani lokaci ma har da kashe-kashe. 

Littafin Gawa Ta ƙi Rami’, yana ɗauke ne da wani labari da aka gina shi akan jigon cin amana, zamba cikin aminci, ɗaukar fansa, da kuma soyayya. Labari ne irin na ýan mafiya, waɗanda suke aikata wasu haramtattun kasuwanci da ba a bayyana takamaimai wane irin kasuwanci ba ne. Amma an nuna yadda Hajiya Abu matar Alhaji Haruna ta shirya wani makirci, inda aka ɗauka ta yi hatsari ta mutu. Mutuwar da ta rikita mijinta ta fitar da shi daga hayyacinsa, da cire masa tunanin kowacce ýa mace. Kodayake abokan cin mushensa irin su Alhaji Tanko Bara’u da Alhaji Kawu Maitangaran da suka ba shi ajiyar wata haramtacciyar dukiya, shi kuma ya bai wa matarsa ajiya, ba su gamsu da rasuwar Hajiya Abu ba. 

Bayan wasu shekaru, Hajiya Abu ta sake bayyana, sakamakon wani ƙullin makirci da abokan mijinta suka shirya mata tun daga Sa’udiyya, inda ta gudu tana gudanar haramtaccen kasuwancin da suka saba yi ita da mijinta, tare da wasu ƙawayenta masu harkar zaman Makka suna rayuwa da takari.

Rayuwa dai ta dagulewa Hajiya Abu, yayin da abokan Alhaji Haruna, suka sanya aka sace yaranta ýammata su biyu, Bilkisu da Hannatu, har da amaryar da ake tsaka da bikinta. Ita ma sabuwar matar Alhaji, wato Zahira ta sa ƙawarta Alawiyya bincike akan asalin wacce ce Hajiya Abu da dalilin da ya sa Alhaji kullum yake cikin kewar tsohuwar matarsa, bai damu da zaman ta da shi ba. 

A ƙarshe dai rayuwar Hajiya ta shiga tsaka mai wuya, Alhaji Haruna, tsohon mijinta, da karnukan farautarsa na can suna nemanta, bayan ya gano ba ta mutu ba. Su ma abokansa da suka yi sanadiyyar dawo da ita Kano suna can suna farautarta, sannan jami’an tsaro suna nemansu duka. 

Littafin mai shafi 219 an yi masa tsari cikin yanayi na babi-babi har tara. An rubuta shi cikin daidaitacciyar Hausa, da salo mai ban sha’awa da riƙe mai karatu. Ga duk wanda ya taɓa karanta littafin ‘ɗa Ko Jika’ na marubuci Bala Anas Babinlata, zai so ya karanta ‘Gawa Ta ƙi Rami’, saboda tsarin da aka rubuta su iri ɗaya ne, sai dai labaran daban-daban ne!

Cikin hikima da basira irin ta fasihan marubuta, Ayuba Muhammad ɗanzaki ya yi ƙoƙarin warware bakin zaren labarin a sauƙaƙe ba tare da ya wahalar da tunanin mai karatu ba, ko kuma ya samu matsalar kubcewar salo ba. Abin da ke nuna lallai an ɓata hankalin dare sosai wajen haɗo kan ɓangarorin labarin da suka gina mana yadda kowanne a cikin taurarin labarin yake ƙulla nasa makircin. 

Sannan akwai wani salon magana da marubucin ya yi amfani da shi wajen ƙawata harshe da jan hankali a shafi na 151 ya birgeni ƙwarai da gaske. Bari ku ga abin da ya rubuta. “Ta saurara don ta ji alamar motsin mutane a kusa da ɗakin, ina ma ita ɓera ce ko kyanwa da ta sakaɗa ta ƙaramar ƙofar tagar da ke can sama ta sulale abinta. Ina ma ita ƙadangaruwa ce da ta bi bangon ɗakin har zuwa sama inda take hango wata ƙofa da hasken rana ya keto ta cikinta ya sauka a fusace a kan fuskarta. Ina ma a ce ita tsuntsuwa ce da sai ta laɓe a bakin ƙofar fita ta ɗane ƙofa da yatsun ƙafarta, idan wani ya buɗe ƙofa sai ta tashi fir! Ta nufi inda take so.”

Duk da ƙoƙarin da marubucin ya yi wajen kyautata rubutunsa, da kiyaye kurakurai masu yawa, na lura da wasu wurare da suka kubcewa marubucin ba tare da ya lura da su ba. Da fatan kuma za a gyara su  nan gaba, a lokacin da aka tashi sake buga littafin. 

Na lura da yadda aka samu ƙalubalen na’ura wajen fitar da haruffan (ƙ) (ɓ) (ɗ) inda aka riƙa musanya su da (ɗ) (ɓ) (ƙ), wanda hakan na iya hana mai karatu jin daɗin karatun a sauƙaƙe. Ya kamata da an samu kwamfiyuta mai amfani da manhajar da take da alƙaluman rubutun Hausa, ko kuma a juya yadda alƙaluman suke, ta hanyar sa wata alama, kamar (‘k) (‘b) (ď), waɗanda za a iya ƙirƙirar su a kowacce na’ura.

A shafi na 37 sakin layi na farko, an yi amfani da kalmar ‘ƙananu shekaru’ a maimakon ‘ƙananan shekaru’. Haka kuma a shafi na 40 sakin layi na farko an nuna cewa, bayan dawowar yaran Hajiya Abu daga makaranta, ‘kowaccensu ta shiga ɗakinta ta canza kaya ta yi wanka’, alhalin a baya a shafi na 28 an bayyana cewa yaran Hajiya za su cigaba da kwana a ɗaki ɗaya ne, saboda ɗaya daga cikinsu, Hanne, ta nuna cewa tana jin tsoron kwana ita kaɗai.

Sannan, an yi ta amfani da sunan ‘Babur mai ƙafa uku’ a maimakon ‘A daidaita sahu’ kamar yadda aka saba faɗa musamman a Kano, inda a nan ne aka shirya labarin.

A shafi na 74 a sakin layi na farko na rubuta ‘ƙata ƙofa’, a maimakon ƙatuwar ƙofa ko wata ƙofa. 

A yayin da ake bayar da labarin Hajiya Abu ta yi tafiyar gaggawa zuwa ƙauyensu ɗansarai, a shafi na 121 sakin layi na huɗu an bayyana cewa, ta isa ƙauyen misalin ƙarfe 10 na dare. Amma sai ga shi a shafi na 122 sakin layi na 3, an rubuta cewa, Hajiya ta zauna har zuwa bayan sallar Isha. Wannan na nuna an samu kuskuren ayyana lokaci, domin kuwa akwai tazara tsakanin sallar Isha zuwa ƙarfe goma. 

A shafi na 137 sakin layi na 4, an yi kuskure wajen rubuta, ‘Ya kamata ta yi gaggawar yi wa hanci tufka tun kafin wankin hula ya kai ta dare.’ A maimakon… yi wa tufkar hanci tun… 

Sai dai labarin ya yi shiru game da yadda aka kaya a ɓangaren Zahira matar Alhaji Tanko wacce ta biya ƙawarta Alawiyya ta yi mata bincike kan dalilin da ya sa Alhajin kasa mantawa da matarsa marigayiya, aikin da ya jefa Alawiyyar cikin tsaka mai wuya. Shin bayan Zahira  ta ji abin da ya faru da ƙawarta wanne matakin ta ɗauka? Me mijinta Alhaji Tanko ya yi mata bayan da ya gano ita ce ta kitsa wannan binciken ƙwaƙwaf da ake yi masa? 

Sannan a ɓangaren Nasir da ya auri ýar wajen Hajiya wato Bilkisu, yaya rayuwarsa ta kasance bayan da aka gano inda matarsa da surikarsa suke? Shin an cigaba da batun auren ne ko sun rabu, bayan da ya gano makircin da mahaifiyar matarsa ta ƙulla? 

Babu shakka labari ya tsaru kuma ya yi daɗi sosai. Ina jinjina ga Malam Ayuba Muhammad ɗanzaki, zakin marubuta, bisa ƙoƙarin da yake yi na ceto harkar rubutun adabi, a lokacin da maza marubuta da dama suka jingine harkar rubutu aka bar wa mata, wasu kuma suka koma rubutun finafinan Hausa. Yana da muhimmanci mu riƙa tallafawa irinsu ta hanyar ƙarfafa musu gwiwa da karanta littattafan da suke wallafawa. 

‘Gawa Ta ƙi Rami’ ɗaya ne daga cikin littattafai goma da marubucin ya rubuta, wanda kowanne ke ɗauke da labari mai bansha’awa, nishaɗi da ilimantarwa. Daga cikinsu akwai ‘Shingen ƙauna’, ‘Haɗin Zumunta’, ‘Fadar So’, ‘Sun ƙi Allah Ya So’, ‘Rayuwar Bilkisu’, ‘Na Ci Amana’, ‘Aure Kan Aure’, ‘Jininmu ɗaya’, da kuma ‘Kurman Hisabi’.

By ukarofi