An bai wa marubuta mata horo kan dabarun inganta rubutunsu

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Cibiyar Nazari da Karantar da Harshen Hausa da Al’adu ta ƙasar Togo tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Muryar Afirka Midiya sun gudanar da wani taron bita na yini biyu, daga ranakun Asabar 18 da Lahadi 19 ga watan Janairu, 2025 domin koyar da marubutan adabi mata zalla wasu dabaru na yadda za su ƙara inganta ayyukansu na rubuce-rubuce.

Taron bitar wanda ya gudana a ɗakin taro na American Space da ke Babban ɗakin Karatu na Murtala Mohammed a Kano, ya samu halartar marubuta mata fiye da talatin da suka fito daga jihohin Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Sakkwato, da Babban Birnin Tarayya Abuja, har ma da wasu daga Kwatano a Jamhuriyar Benin.

Taron bitar da aka yi wa taken, ‘Labaranmu Abin Alfaharinmu’ ya mayar da hankali ne wajen koyar da marubutan dabarun rubutun gajerun labarai, ƙa’idojin rubutu, rubutun tarihi da kuma ƙa’idojin fassara. ƙwararrun masana ilimin adabi irinsu Dr Tijjani Shehu Almajir, Dr Zainab Umar Saleh, Dr Faruk Lawan Da’u, da kuma Yasir Ibrahim Kalla, waɗanda suka fito daga jami’o’in Nijeriya daban-daban, su ne suka jagoranci horarwar da aka yi.

Dr Tijjani Shehu Almajir shi kuma ya koyar da ‘Dabarun Rubuta Gajerun labarai’. Ita kuma Dr Zainab Umar Saleh ta koyar da su, ‘Hanyoyin Inganta Rubutun Tarihi’. Yayin da Dr Faruk Lawan Da’u ya yi musu bita kan, ‘ƙa’idojin Rubutu. Sai kuma, Yasir Ibrahim Kalla ya koyar da mahalarta taron, ‘Dabarun Fassara’. 

Shugaban kamfanin Muryar Afirka Midiya, Malam Muhammad Rabi’u Abu Hidaya, wanda suka jagoranci shirya taron ya ce, gamayyar cibiyar da ƙwararrun kamfanin suna gudanar jerin harkoki ne da suka shafi raya al’adun Hausawa da tarihinsu a mataki daban-daban, kamar yadda a baya aka fara daga ƙasar Togo, inda aka gudanar da bikin baje-kolin abincin Hausawa, da wasu taruka na raya al’adu.

Abu Hidaya ya bayyana manufar taron bitar da cewa, ‘Muna so ne mu inganta fikira da fasahar marubutanmu, da kuma farfaɗo da tasirin rubutu a yau. Bisa la’akari da yadda yanayin rubutun adabi a wannan lokaci yake samun koma baya, musamman yadda marubutan suka karkata wajen rubutu kan jigon soyayya kaɗai. Sai muka yi wani tunani kan cewa, me za mu yi wanda zai dace da manufar gina wannan cibiya na farfaɗo da al’adu da tarihin al’ummar Hausawa. Shi ne muka gano cewa ta hanyar rubuce-rubuce ne za mu iya yin wani abu da zai nuna cewa, duniyar mu tana nan, kuma marubutanmu na daga cikin ƙashin bayan al’umma, wajen taskance tarihi da al’adu, waɗanda al’ummomi masu zuwa nan gaba za su san kafin su akwai wata al’umma da ta wanzu. 

“Shi ya sa muka mayar da hankali wajen ba su horo kan abin da ya shafi tarihi da fasara, domin su koyi yadda ake juya tunanin wasu al’umomin da zamantakewar su ta yadda za ta amfani cigaban rayuwar Hausawa, kamar yadda su marigayi Dakta Abubakar Imam suka yi a lokacin su. Sannan kuma an koya musu dabarun gajerun labarai, don inganta rubuce-rubucen adabi da nishaɗi.”

Ya ƙara da cewa, “Daga bitar da aka shiryawa marubuta mata, za su samu ilimin yadda za su sarrafa basirarsu a matsayin wata hanya ta taskance tarihi da hanyoyin samun shigar kuɗaɗe. Sannan za su riƙa samun wasu ayyuka da cibiyar za ta riƙa yi musu hanya suna gudanarwa.”

Shi ma Dr Faruk Lawan Da’u ɗaya daga cikin ƙwararrun da suka gudanar da bitar ya bayyana cewa, “Mu Hausawa mu muke da labarin da za mu faɗa, don har yanzu duniya na son ta ji wanene Bahaushe?  Daga bitar da aka yi har an samu wasu zaƙaƙurai waɗanda suke sha’awar rubutu, kuma har ma wasu daga cikinsu sun fara, sun ma taka wani mataki na nasara. Shi ne muke so mu ɗora su a hanyar da nan gaba idan sun yi rubutu, sai duniya ta ce yaya haka ya faru?”

Hassana Suleiman Isma’il shugabar ƙungiyar Women of Words, wacce mambobinta suka amfana da wannan bita da aka gudanar ta bayyana matuƙar farincikinta da samun wannan muhimmiyar dama da ƙungiyarsu ta yi, watanni kaɗan da kafuwarta. Kasancewar dama daga cikin manufofin kafa ƙungiyar tasu sun yi alƙawarin samar da damarmaki na gudanar da horo da bita don bunƙasa gogewar mambobin a harkar rubutun adabi da bincike. 

Tun da ƙungiyar ta gano shirin da Cibiyar Nazari da Karantar da Harshen Hausa da Al’adu ta ƙasar Togo tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Muryar Afirka Midiya suke yi na samar da horo ga mata marubuta kan harkokin inganta rubuce-rubuce da al’adun Hausawa. Sai suka ga ai faɗuwa ce ta zo daidai da zama, domin kuwa manufofin su sun zo ɗaya. 

Ta hanyar tattaunawa da wakilinsu, Malam Muhammad Rabi’u Abu Hidaya, ƙungiyar ta samu amincewar su, da damar gabatar da mambobinta don su amfana da horarwar da za a yi a Kano.

Ta ce, “Alhamdulillah, mun samu horo sosai kuma mun kwashi romon ilimi yadda ya kamata. Muna godiya ƙwarai da gaske da samun wannan babbar nasara da ƙungiyar mu ta yi. Ni a karan kaina na samu ilimi da yawa wanda a baya ban sani ba, musamman ilmin fassara, wanda a bayan ba ni da sha’awa ko kaɗan a fannin, kuma yana daga cikin abin da na ƙi jini a fannin aikin jarida. Amma yanzu bayan wannan horo da muka samu an buɗa min ilmin abin an kuma busa min numfashin yin rubutu a fannin. Haka kuma, a ɓangaren tarihi ma sam ban taɓa kwatanta rubutu akai, ko kuma sha’awar hakan da abin da ya shafe shi ba. Hasalima ban san matakan yin rubutu a fannin ba, amma kuma yanzu sanadin wannan bita yanzu na sani.”

Fauziyya Sani Jibrin, ita ma mamba ce a ƙungiyar WOW, bayan godiya da ta yi ga jagororin wannan bita, ta kuma nuna jindaɗinta da wannan gagarumar dama da ta samu. Ta bayyana cewa, “Na ƙaru da abubuwa masu tarin yawa waɗanda za su taimaka min wurin inganta rubutuna. Na ƙara fahimtar ƙa’idojin rubutu, da dabarun gina gajeren labari. Na kuma ƙara sanin salo, azanci, da kuma karin magana, da hanyoyin da ake bi a yi wa labari ado da kwalliya. Ina sa ran samun kuɗaɗe masu tarin yawa, daga ayyukan da zan yi da alƙalamina. Kuma zan amfanar da al’umma sosai da ilimin da na samu. Ina fatan samun ɗaukaka a Duniyar Marubuta da Makaranta, har ma da Manazarta, in sha Allah.”

By ukarofi