An sami tarzoma a hedikwatar jam’iyyar PDP yayin da aka ba hammata iska a taron hukumar amintattu (BoT) na jam’iyyar da aka gudanar a ranar Laraba. Rikicin ya fara ne bayan zuwan Ude-Okoye, wanda ya shiga ɗakin taro amma ya ƙi gaisawa da abokin hamayyarsa, Samuel Anyanwu. Daga bisani, wasu da ake zargi da ‘yan daba ne suka tilasta wa Ude-Okoye ficewa daga taron, lamarin da ya haifar da cece-kuce.
Bayan fitar da shi, Ude-Okoye ya nuna fushinsa yana zargin cewa an hana magoya bayansa shiga hedikwatar jam’iyyar, yayin da na Anyanwu suka sami damar shiga. Wannan rikici ya ƙara dagula lamarin da tuni ya zama batu mai sarkakiya tun bayan da Anyanwu ya bar kujerar sakataren jam’iyya domin yin takarar gwamnan Imo, wanda ya faɗi.
A watan Disamba na shekarar da ta gabata, wata kotun ɗaukaka ƙara a Enugu ta tabbatar da Ude-Okoye a matsayin sahihin sakataren PDP, tare da cire Anyanwu daga muƙamin. Sai dai Anyanwu ya garzaya kotu domin neman dakatar da aiwatar da hukuncin tare da ɗaukaka ƙara, wanda ya ƙara tsananta rikicin cikin gida na jam’iyyar.
