
Daga BELLO A. BABAJI
A sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin Samuel Anyanwu da Ude-Okoyes kan tabbatar da sahihin Sakataren PDP na ƙasa, jami’an tsaro sun karɓe ragamar kula da Sakatariyar jami’yyar.
Jami’an sun haɗa da sojoji, ƴan sanda, jami’an tsaro na ƙasa da na Civil Defense.
Rikicin ya soma ne a lokacin da Anyanwu da Ude-Okoyes suka halarci zaman Hukumar Amintattun (BoT) ta jami’yyar, inda wani mataimakin Samuel Anyanwu ya Ude-Okoyes da ƙarfi daga wajen taron jim-kaɗan bayan wata ganawar sirri.
Lamarin da ya haifar da hatsaniya tsakanin ɓangarorin biyu, wanda har ya kai ga jami’an tsaro sun shiga tsakani.
Batun wane ne sahihin Sakataren jami’yyar ya fara samun tsaiko ne tun lokacin da Anyanwu ya tafi tsayawa takarar kujerar gwamnan Jihar Imo, wadda ya yi rashin nasarar samu.
Kasancewar baya nan, sai jigogin PDP na yankin Kudu maso Gabas suka bada sunan Ude-Okoyes a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
A ƙoƙarinsa na dawo wa muƙaminsa ne jam’iyyar PDP ta shiga halin rikici inda har Kotun Ɗaukaka ƙara a Jihar Enugu ta yi hukuncin cire Sanata Anyanwu daga muƙamin tare da tabbatar da Ude-Okoyes a matsayin sahihin sakataren.
