
Daga BELLO A. BABAJI
Jam’iyyar APC ta tabbatar da korar tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola daga jami’yyar bayan zargin sa da yi mata zagon-ƙasa.
Aregbesola tsohon ministan harkokin cikin gida kuma jagoran ƙungiyar ƴaƴan jam’iyyar mai suna Omoluabi Caucus a jihar, wadda aka zarge ta da taimaka wa rashin nasarar da jam’iyyar ta yi a zaɓen gwamnan Osun a shekarar 2022.
A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a mataki na ƙasa, ta tabbatar da kokar ɗan siyasar bayan saɓa wa dokar jam’iyyar ta matakan ladabi ga mambobi.
Tuni dai jami’yyar NNPP ta nemi Aregbesola da ya shigo cikinta don ci-gaban jihar, kamar yadda Shugaban jami’yyar, Dakta Tosin Odeyemi na jihar ya bayyana a wata sanarwa.
Ya ce NNPP jami’yya ce ta al’umma ganin yadda Gwamna Abba ke yi wa Jihar Kano ƙoƙari a Gwamnatinsa.
Ya ƙara da cewa, kasancewar Aregbesola tsohon gwamna ne kuma gogaggen ɗan siyasa, za a amfana da shi sosai matuƙar shi da ƴan ɓangarensa suka amince da tayin NNPP.
