Daga USMAN KAROFI
Dakarun Hukumar EFCC sun yi dirar mikiya a gidan tsohon shugaban hukumar kula da inshorar lafiya ta ƙasa NHIA, Farfesa Usman Yusuf, da ke Abuja, inda suka kama shi.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an da ke ɗauke da bindigogi sun kama Farfesa Yusuf ne a gaban iyalinsa da misalin ƙarfe 4:46 na yamma a ranar Laraba, 29 ga Janairu, 2025. An ce an ɗauke shi zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.
Duk da cewa ba a bayyana dalilin kama shi ba, wasu majiyoyi sun ce yana da alaƙa da ayyukansa lokacin da yake shugabancin NHIS. A shekarar 2019 ne tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya cire shi daga muƙaminsa bayan wani kwamitin bincike ya zarge shi da yin sama da faɗi da naira miliyan 919.
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya ce zai tabbatar da gaskiyar lamarin amma bai dawo da amsa ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.
