JAMB ta fitar da ranar fara rajistar 2025

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya (JAMB) ta sanar da sauya ranar fara rajistar jarabawar UTME ta 2025. A cewar hukumar, rajistar da aka shirya fara ranar Juma’a, 31 ga Janairu, za a fara ta ne a ranar Litinin, 3 ga Fabrairu. Kakakin JAMB, Dr. Fabian Benjamin, ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin yin wasu muhimman gyare-gyare a tsarin rajistar.

JAMB ta bayyana cewa ɗaya daga cikin dalilan jinkirin shi ne dakatar da wasu shirye-shiryen karatun lauya a wasu jami’o’i, wanda hukumar kula da Ilimin lauya ta ƙasa ta sanar da ita. Haka kuma, hukumar ta gano cewa wasu cibiyoyin rubuta jarabawa na CBT sun yi amfani da wasu dabaru na yaudara don samun amincewa, wanda hakan ya buƙaci sake dubawa da cire su daga jerin cibiyoyin da za a yi rajista a cikinsu.

Hukumar ta JAMB ta nemi afuwar ɗalibai da iyayensu kan wannan canji, tana mai cewa tana ƙoƙarin tabbatar da tsarin rajistar da ba zai fuskanci wata matsala ba. Ta kuma buƙaci ɗalibai su shirya domin fara rajista a ranar Litinin, 3 ga Fabrairu, domin samun damar zana jarabawar UTME ta bana.

By ukarofi