Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano
An bayyana cewa a ƙokarin amsa kiran Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf na tsaftace muhalli domin inganta lafiyar al’umma musamman kasuwanni da masana’antu da unguwani da gidaje domin yaƙar ambaliyar ruwa da ke zama sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyi a shekaru da dama da suka gabata a Nijeriya da ma wasu ƙasashen na duniya ne dalilin da ya sa shugabancin kasuwar ya ƙaddamar da yashe magudanar ruwa masu tsawon mita 1500 a kasuwar Beruit Road, inda za su ɗauki mako guda suna wannan aiki don kawo cigaba a wannan kasuwa ta fuskar tsaftacen ta kamar dai yadda shugaban riƙo na wannan kasuwa Ambasada Kabir Musa wanda aka fi sani da KABS Communication ya bayyana a lokacin gangamin ƙaddamar da yashe magudanan ruwa na kasuwar da aka ɗauki kimanin shekaru uku ba a yashe ba, wanda magudanan ruwan suka cika cunkus.
Haka kuma ya bayyana cewa ganin yadda gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa sabon kwamishinan ciniki da masana’antu na Kano Alhaji Wada Sagagi ya sa suka samu kyakkyawar alaƙa da fahimta da kwamishinan kasuwanci na Kano wanda kuma wannan ya sa suka zage damtse wajen ganin duk wani abu da zai kawo cigaba a wannan kasuwa da ma kasuwannin Kano na tabbatar ‘yan kasuwan Kano a shirye suke su bai wa ma’aiakatar ciniki da masanaantu da gwamnatin Kano a kowanne lokaci, don haka za mu cigaba da inganta kasuwar waya ta Beruit Road da ke Kano ‘yan kasuwa da ma’akatanmu a kodayaushe.
Shi ma Malam Nura Yusuf Abubakar Kabo jami’in hulɗa da jama’a na kasuwar Beruit Road kira ya yi da ‘yan kasuwar Beruit Road kan su ci gaba da bada haɗin kai domin samun nasara a wannan aiki na yashe magudanar ruwa da sauran abubuwa na cigaba da Ambasa Kabiru Musa ya zo da su da samun nasara a ɗan ƙanƙanin lokaci da kama ragamar shugabancin riƙo.
Haka shi ma Khalid Muhammad babban jami’in tsaron kasuwar ya ce wannan ba ƙaramin alkairi ba ne da wannan kasuwa ta samu a wannan lokaci domin su kansu ma’aikatan tsaro na wannan kasuwa da ake yashe magudanar ruwa alheri ne babba inda kuma ya yaba wa shugaban riƙon ya yi kan haɗin kai da suke samu daga gare shi da sauran ‘yan kasuwar Beruit Road Kano.
