Har yanzu Nijeriya ce mafi ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka, inji Bankin Duniya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Daraktan Bankin Duniya na Nijeriya, Dakta Ndiame Diop ya tabbatar da cewa har yanzu tattalin arziƙin Nijeriya shi ne ke kan gaba a Nahiyar Afirka bisa abubuwan da ta mallaka na GDP duk da ƙalubalen da ta ke fuskanta.

A lokacin da ya ke magana a taron masu-ruwa-da-tsak da cibiyar ci-gaba a zuba hannun-jari (CPSD) a Abuja ranar Alhamis, Daraktan ya ce a yayin da Nijeriya ke samun ƙarancin zuba hannun-jari daga ƙasashen waje (FDI) musamman idan aka kwatanta ta da ƙasashen Indonesiya da Afrika ta Kudu, hakan bai sanya tattalin arziƙinta faɗuwa ba.

Ya ce nan da mako guda za a fitar da rahoton CPSD wanda zai bayyana tasirin ɓangaren mallaka ga tattalin arziƙi da kuma gano matsaloli, waɗanda magance su zai taimaka wa haɓakarsa.

Dakta Diop ya ƙara da cewa gyare-gyare ga harkar tattali sun taimaka wajen kawo sauyi da bada damar zuba hannun-jari da sauƙaƙe harkokin kasuwancin ƙasashen waje.

Ya bayyana sauye-sauyen a matsayin ababan da za su janyo ra’ayoyin masu zuba hannun-jari da dama da samar da ayyuka.

Ya bada misali da ɓangaren Fasahar Sadarwa ta ICT, wadda ta samar da damar zuba hannun-jari na Dala biliyan 4, wanda ya samar da ayyuka sama da 200,000.

Haka ma gyare-gyare a kasuwancin noma na Agribusiness za su samar da damar zuba hannun-jari na Dala biliyan 6 da samar da ayyuka sama da 275,000.

Kazalika, ya ce Majalisar Zartarwar ta ɗauki matakin amfani da damammakin ɓangaren inda ta ke amfani da damar shirin tallafin Bankin Duniya.

By Babaji