
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ƙirƙiro tsarin sabonta fasfo a Turai ba tare da zuwa ofishin jakadanci ko wata cibiya ba, wanda hakan zai bai wa ƴan Nijeriya dake zaune a Nahiyar damar sabonta fasfo ɗinsu ta yanar gizo.
Ministan Harkokin Cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo a wata ganawa da manema labarai a Abuja ya bayyana hakan, inda ya ce sabon tsarin ya kawo ƙarshen bin hanyoyi masu tsauri wajen sabontawa ga al’umma.
Ya ce hakan na zuwa ne sakamakon ƙoƙarin gwamnati na bunƙasa hanyoyin kula da ƴan Nijeriya dake rayuwa a ƙasashen waje a ƙarƙashin ajandar Shugaba Bola Tinubu na sabonta ƙasa.
Ya ƙara da cewa hakan zai taimaka wajen rage adadin lokacin da ake ɗauka a yayin sabonta fasfo, ya na mai cewa tsarin da ƙasashen da suka ci-gaba suke bi kenan, kamar Canada da wasu ƙasashe.
Kazalika, ya ce gwamnati za ta cigaba da ƙoƙarin sauƙaƙe wa al’umma hanyoyin amfani da ababen more rayuwa a ko’ina suke a duniya.
