Daga ABDULLAHI Muhammad a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanar da shirin sa na mai da kasuwar Mai’adua a ƙaramar hukumar Mai’adua irin ta zamani domin bunƙasa samun hanyoyin kuɗaɗen shiga a jihar.
.
Malam Dikko Raɗɗa ya faɗi hake na a garin Mai’adua a lokacin da yake ƙaddamar da aikin hanya a yankin.
Ya ce da an kammala aikin kasuwar za ta taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da inganta hanyoyin samun kuɗaɗen shiga a jihar.
A cewar Dikko Raɗɗa aikin hanyar mai tsawon kilomita 4.5 zai ci kuɗi Naira biliyan 1.46.
“Aikin hanyar zai tashi daga Mai’adua zuwa Daba ta miƙa har Botsotsuwa ta ƙarasa iyaka da Nijar.
Kafin nan gwamnan ya ƙaddamar da aikin faɗaɗa wasu hanyoyi guda biyu masu tsawon kilomita 30 da zasu ci kuɗi Naira biliyan 4.6.
Hanyoyin kuwa sun haɗa da hanyar da ta tashi daga sheme zuwa Faskari da wanda ta tashi daga kasuwar mata Funtua zuwa Ɗandume.
Akwai wasu hanyoyin da ya ƙaddamar a sassa daban-daban a faɗin jihar ƙarƙashin shirin bankin duniya na bunƙasa hanyoyin karkara da inganta kasuwancin amfanin gona (RAAMP).
