
Daga BELLO A. BABAJI
Matashin mai suna Sa’idu Abdulrahaman mai kamfanin hoto na Sp Photography ɗan asalin garin Potiskum a Jihar Yobe, ya ɗauki hotona 897 ne acikin sa’a guda wanda hakan yasa ya kafa tarihi a fannin ɗaukar hoto a mataki na duniya.
Haka kuma shi ne mutum na farko da ya fara kafa tarihi a fannin daga Arewacin Nijeria.
Hakan yasa ya shiga kundin tarihi na ‘Guinness World Records’ inda suka ba shi takardar shaidar a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin nuna muhimmancin hoto a duniya.

A lokacin da ya ke magana da manema labarai, Sa’idu ya ce burinsa shi ne ya ga matasa suna shiga harkar ɗaukar hoto saboda irin alkairi da bada gudunmawa da ke cikinsa.
Ya kuma ƙudiri aniyar koya wa masu tasowa sana’ar don samun abin dogaro da kai.
Matashin ya yi kira ga matasa da su zama masu himma da jajircewa kan duk wani abu da suka saka a gaba ko kuma suke son cimmawa, domin ita nasara ba ta samuwa cikin sauƙi matuƙar ba a jajirce ba.
