
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙudirorin gyaran dokokin haraji guda huɗu da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa majalisa a shekarar da ta gabata ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai a ranar Laraba.
Watanni shida kenan da Shugaban ƙasar ya miƙa ƙudirorin don tantancewa biyo bayan sahalewar Kwamitin Tsare-tsaren kuɗi da Gyare-gyaren Haraji ƙarƙashin jagorancin Taiwo Ayo-Dele.
Ƙudirorin sun haɗa da na ƙudirin harajin Nijeriya na 2024 da ƙudirin harajin rajista da ƙudirin samar da hukumar haraji da kuma ƙudirin samar da hukumar hukumomin haraji.
Kasancewar ƙudirin ya tsallake karatu na biyu, yanzu kuma sai gabatar da shi a gaban alƙali domin tantancewa ta ƙarshe.
A baya dai an yi ta samun cecekuce daga ƴan ƙasa ciki har da gwamnonin arewa da ɓangaren ƴan adawa, waɗanda suka buƙaci a janye batun daga majalisar.
Saidai, a ranar Laraba an samu da dama daga cikin ƴan majalisar da suka goyi bayan ƙudirin dokar harajin duk cewa an samu ɗaya daga cikinsu mai suna Sada Soli, wanda ya yi fargabar wasu layuka acikin ƙudirin ka iya cin karo da wasu dokokin kundin 1999, ya na mai kira da a yi gyara akansu gabannin aiwatarwa.
