Rumbun lantarki ya lalace karo na farko a 2025

Spread the love

Rumbun wutar lantarki na ƙasa ya sake faɗuwa a ranar Laraba, wanda ya jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin duhu. Wannan shi ne karo na farko da hakan ya faru a shekarar 2025.

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Ikeja (Ikeja Electric) ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa matsalar ta afku da misalin ƙarfe 11:34 na safe. Kamfanin ya ce suna aiki tare da hukumomi masu alaƙa don dawo da wutar lantarki cikin gaggawa.

Haka nan, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) shima ya tabbatar da matsalar, yana mai cewa yankunansu sun fada cikin duhu sakamakon wannan tangarɗa. Kamfanin ya tabbatar wa abokan hulɗa cewa ana ƙoƙarin dawo da wuta a hankali bayan faruwar lamarin.

Wannan matsala ba sabon abu ba ce, domin a shekarar 2024, rumbun wutar lantarki ya faɗi har sau 12. Wata shahararriya a X mai bibiyar harkar wutar lantarki ta bayyana cewa an samu “tangarda a rumbun lantarkin” kafin tsakar rana, wanda ya haddasa katsewar wuta a wasu sassan ƙasar.

By ukarofi