Daga USMAN KAROFI
Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta umarci ma’aikata da sauran ‘yan ƙasa masu son haɗin kai da su ƙaurace wa amfani da kamfanonin sadarwa irin su MTN, Airtel, da Glo daga karfe 11:00 na safe a ranar Alhamis, 13 ga Fabrairu, 2025, sakamakon ƙarin ƙuɗin sadarwa.
NLC na buƙatar a gaggauta janye ƙarin farashin. Shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero, da sakataren ƙungiyar, Emmanuel Ugboaja, ne suka bayyana hakan a wata sanarwa da suka fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta bayyana cewa, “Mun buƙaci a janye wannan ƙarin farashi nan take, kuma dole ne a koma ga tsohon farashin har sai kwamitin da ke tattaunawa kan lamarin ya kammala aikinsa da cimma matsaya. A matsayin matakin farko, mun umurci ma’aikata da sauran ‘yan ƙasa da su ƙauracewa amfani da layukan sadarwa na MTN, Airtel, da Glo daga ƙarfe 11:00 na safe zuwa 2:00 na rana, kowace rana, daga ranar 13 ga Fabrairu har zuwa karshen watan.”
Cikakkun bayanai na tafe…
