MƊD ta saki Dala miliyan 5 a shirin kare ambaliyar ruwa a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mai tsara taimako na gaggawa na Majalisar Ɗinkin Duniya, Tom Fletcher, ya bada Dala miliyan biyar daga asusun ‘Central Emergency Fund’ (CERF) don ɗaukar mataki na wucin-gadi ga ambaliya da ake samu a Nijeriya.

Mai tsara ayyukan agaji na MƊD a Najeriya, Mohamed Malick Fall, ya fitar da sanarwar a ranar Laraba, a Abuja.

Mista Fall ya ce “Yin tsammani da kuma yin aiki kafin matsaloli…. Yana kuma taimaka wa wajen kare abincin mutane wanda kuma yana rage rashin lafiyarsu.”

“A cikin yanayin duniya wanda ake kare da rage kuɗaɗe don ayyukan jin ƙai, wannan matakin yana da matuƙar muhimmanci domin baya rage mafi munanan tasirin gaggawa kawai, yana kara taimakawa wajen rage tsadar kudin amsa ga jin ƙai.”

Rabon dala miliyan 5 na CERF yana tallafawa ƙoƙarin da gwamnati ke jagoranta ta hanyar ƙungiyar aikin da ake fuskanta a gaba.

Haka kuma, ƙungiyar aikin tana haɗa muhimman hukumomi ciki har da Hukumar Yanayi ta Najeriya (NiMET), Hukumar Hidimar Ruwa ta Nijeriya, da Hukumar Kula da Bala’o’i ta Ƙasa ƙarƙashin kulawar Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa. Wannan yana cikin haɗin gwiwa da Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya na Kula da Ayyukan Jin ƙai (OCHA).

A Duniya gaba ɗaya, OCHA wanda ke sarrafa CERF da Kuɗaɗe na Ƙasashe (CBPFs) kamar Asusun Jin ƙai na Najeriya (NHF), yana jagorantar aikin da aka tsinkayo na gaba da taimaka wa miliyoyin mutane ta hanyar magance haɗari irin su ambaliyar ruwa, fari, guguwar iska da kuma cutar amai da gudawa.

A watan Oktoba na shekarar 2024, CERF ta saki Dala miliyan 5 don ƙara yawan amsa ambaliyar ruwa da magance buƙatun gaggawa a jihohin Borno da Bauchi a arewa maso gabashin Nijeriya, da Jihar Sakkwato a arewa maso yamma.

Kuɗaɗen CERF sun taimaka tare da rabon Dala miliyan 6 daga NHF (wanda ya haɗa da Dala miliyan 2 don aikin tsinkaya wanda aka fitar tare da manyan ambaliyar ruwa da suka ɗaiɗaita kusan mutane 400,000 a Borno).

Dai-dai da hasashen Yanayi na 2025 na NiMET, ana sa rai cewa damina zai fara a jihohin arewa kamar Bauchi, Borno, Jigawa, Kano, Katsina, Sakkwato, Yobe da Zamfara, daga farkon Yuni zuwa Yuli 2025.

Wannan lokacin ya dace da lokacin yunwa (lokaci tsakanin girbi) inda rashin abinci da ƙarancin abinci suke ƙaruwa tare da ambaliyar ruwa da yaɗuwar cututtuka irin su amai da gudawa.

Kazalika, shirye-shiryen da suka dace a kan waɗannan haɗurran na iya yiwuwa saboda suna da matukar muhimmanci ga al’umma.

Shirin Buƙatun Jin Kai da Amsar Gaggawa na Nijeriya na shekarar 2025 (HNRP), ya fitar da wata hanya mai ma’ana ta tsinkaya ta hanyar sadaukar da kashi 5 cikin 100 (dala miliyan 45) daga jimillar buƙatun (dala miliyan 910) don aikin tsinkaya.

Wannan rabon kuɗaɗe na CERF ya wakilci kawai kashi 11 cikin 100 na buƙatun don aikin tsinkaya. Ana buƙatar ƙarin kuɗi cikin gaggawa don ƙara yawan aikin.

By Babaji