Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jama’ar jihar Neja sun ce ‘yan bindigar da aka yi sulhu da su a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna na shiga garuruwansu suna aikata ɓarna sannan su koma inda suka fito.
Hon. Zubairu Isma’il Zanna, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja ya ce sulhun na jihar Kaduna bai zamo alheri ga jama’arsa ba.
A hirarsa da BBC, Hon Zanna ya ce kafin sulhun a jihar Kaduna, jama’arsa na zaune lafiya amma yanzu sun tsinci kansu cikin hare-haren ‘yan bindigar, waɗanda yanzu haka suke riƙe da mutane 132 da suka kwasa daga ƙauyukan jihar Neja.
“An samu tsawon watanni ba a samu irin wannan matsala ba, sai yanzu da aka yi sulhu da ‘yan bindiga a Birnin Gwari, tun daga lokacin suke gangarowa yankin jihar Neja, dajin Alawa nan suke zuwa su laɓe su ɗebi mutane su wuce,” cewar Hon Zanna.
ɗan majalisar ya ce sun gabatar da ƙuduri domin ganin gwamnatin tarayya da ta jiha sun ƙara tura jami’an tsaro yankunan domin shawo kan matsalar, “an daukar mana mutane 132 yawancinsu mata da ƙananan yara.”
Zanna ya ce ana sanar da su lokaci da kuma hanyoyin da ‘yan bindigar ke bi domin kai hare-hare, lamarin da ya sanya suka san daga inda suke fitowa.
A kwanakin baya, gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana wa BBC dalilan da suka sanya gwamnatinsa ta amince ta yi sulhu da ‘yan fashin daji a jihar yayin da jihohin da ke maƙwaftaka suka yi watsi da irin wannan tsari.
Lamarin da al’ummar yankunan da rashin tsaro ya fi shafa, kamar Birnin Gwari da Giwa da ƙauyukan ƙaramar hukumar Igabi suka ce ya kawo musu kwanciyar hankali.
Uba Sani ya ce tun farko al’ummar yankunan da suka fi fama da matsalar tsaron ne suka buƙaci a yi zaman sasanci da ‘yan bindiga, inda gwamnati ta duba sannan ta yanke shawarar amincewa da hakan.
Matsalar ‘yan fashin dajin wadda ta addabi jihoin arewa maso yammacin Nijeriya ta tursasa wa manoma barin ƙauyuka, lamarin da ya sanya albarkatun noma da ake samu ya yi ƙasa, wanda masana suka bayyana cewa ya taimaka wajen haifar da tashin farashin kayan masarufi.
Wani abu da ke sanya al’umma a yankunan da ke fama da rashin tsaro na Nijeriya yin ɗari-ɗari da batun yin sulhu da ‘yan fashin daji shi ne batun ɗorewar al’amarin.
A shekarun da suka gabata an gwada yin sulhu a wasu yankunan ƙasar da ‘yan fashin dajin, sai dai lamarin bai ɗore ba.
Baya ga ƙauyukan da suka sha kwatanta irin yin hakan, wani babban misali shi ne sulhun da gwamnatin jihar Zamfara ta taɓa yi da ‘yan fashin daji, lamarin da ya rushe daga baya.
Matsalar rashin tsaro sanadiyyar ‘yan fashin daji a arewa maso yammacin Nijeriya ta haifar da asarar ɗimbin rayuka da kuma tagayyara al’umma da dama.
Lamarin ya fi addabar jihohin Kaduna, da Katsina da Zamfara da Sakkwato da kuma Neja.
Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa tana bakin ƙoƙarinta wajen shawo kan matsalar.
Sai duk da nasarorin da ta samu a baya-bayan nan, ‘yan fashin na ci gaba da tsananta wa al’umma ta kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
