
Daga BELLO A. BABAJI
Jamhuriyar Nijar ta gabatar sabon tsarin shige-da-fice na ƙasarta, wanda ke haramta wa ƴan Nijeriya shiga ƙasar da fasfo ɗin ECOWAS.
Hakan na nufin fasfo na ƙasa-da-ƙasa shi ne kaɗai karɓaɓɓe a yayin shiga ƙasar.
Hakan ya biyo bayan fita daga Ƙungiyar Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS ) da Nijar ta yi tare da Mali da Burkina Faso.
Lamarin da ya haifar da ƙalubale ga ƴan kasuwa da ke zirga-zirga tsakanin iyakokin Nijeriya da Nijar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, wani ɗan kasuwa da ke tafiye-tafiye a tsakanin ƙasashen biyu mai suna Mansur Abdullahi, ya tabbatar da batun, inda ya ce tuni waɗanda ba su fasfo ɗin ƙasa-da-ƙasa suka yi ta juyawa sakamakon ƙin karɓar na ECOWAS da jami’an tsaro ke yi a iyakokin.
Hukumomi a Nijar sun tirje akan sai dai fasfo ɗin ƙasa-da-ƙasa ne za a karɓa, wanda hakan ya sabbaba shiga mawuyacin hali ga ƴan kasuwa da matafiya.
Wani direban kabo-kabo mai suna Abubakar Isa, ya zargi jami’an iyakokin a Nijar cewa suna amfani da damar hakan wajen musguna wa al’umma, inda suke karɓar CFA 5,000 zuwa 10,000 daga waɗanda ke da na ECOWAS don ba su izinin wucewa.
Hukumar ECOWAS ta ce ba ta san da batun tsarin sanya takunkumin da Nijar ta yi ba akan masu fasfo ɗin ECOWAS, kamar yadda jami’in hulɗa da jama’arta, Joel Ahofodji ya bayyana.
