
Daga BELLO A. BABAJI
Mai bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan harkar Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribaɗu ya miƙa mutane 59 da aka ceto daga hannun ƴan bindiga a sassan daban-daban na Kaduna ga gwamnatin jihar.
Da ya ke magana yayin miƙa mutanen a ofishinsa dake Abuja, Ribaɗu ya ce an ceto su ne ƙarƙashin atisayen haɗin-gwiwa tsakanin jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da hukumomin Leƙen asiri da sauransu.
Ya kuma ce, ceto mutanen na nuna yadda Shugaba Bola Tinubu ke jajircewa wajen tabbatar da tsaro a Nijeriya.
