Babbar kotun Kano ta hana CBN da RMAFC riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Babbar kotun Kano ta bada umarni na dindindin ga gwamnatin tarayya kan riƙe wa ƙananan hukumomin Kano 44 kuɗaɗen su.

Mai shari’a Musa Ibrahim Ƙaraye ne ya bada wannan umarni a jiya Litinin, bayan ƙarar da wasu wakilan ƙananan hukumomi suka shigar don kare ƴancin su na karɓar kuɗaɗe daga gwamnatin tarayya.

Waɗanda su ka shigar da ƙarar sun hada da shugaban ƙungiyar NULGE, Ibrahim Muhd da Ibrahim Uba Shehu da Ibrahim Shehu Abubakar da Usman Isa da Sarki Alhaji Kurawa da kuma Malam Usman Imam.

Waɗanda a ke ƙara sun haɗa da Akanta Janar na ƙasa, Babban Bankin Ƙasa, CBN da ‘Revenue Mobilisation Allocation and Fiscal Commission,(RMAFC)’ da ƙananan hukumomi 44 na Kano, bankin UBA da Access da kuma wasu bankuna shida.

Rahotanni na cewa shari’ar ta samo asali ne bayan da jam’iyyar adawa ta APC ta nemi kotu da ta dakatar da rabon kuɗaɗen ƙananan hukumomi, bisa zargin cewa an tafka maguɗi a zaɓen ƙananan hukumomin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) ta gudanar a watan Oktoba 2024.

Jam’iyyar APC ta shigar da ƙarar hukumomi da dama na Gwamnatin tarayya da na Jiha, ciki har da Babban Bankin Ƙasa na (CBN), Kwamitin Raba Kuɗaɗen Tarayya (FAAC), da kuma dukkan ƙananan hukumomi 44 na Kano.

To sai kuma, kotu ta yanke hukunci cewa ƙananan hukumomi na da ƴancin karɓar kuɗaɗen su, kuma ta haramta wa Gwamnatin tarayya ko wata hukuma hana rabon wadannan kudi.

Da ya ke magana bayan hukuncin, lauyan da ya wakilci ƙananan hukumomi 44, Barrister Bashir Wuzirchi, ya bayyana cewa wannan nasara ce ga Jihar Kano.

“Mun shigar da wannan ƙara ne domin kare Kano daga masu son hana ci gaban jihar ta hanyar riƙe kudaɗen ƙananan hukumomi.

By ukarofi